An Fadi Illolin Shigar Amurka Yaki da Boko Haram da Sauran 'Yan Ta'adda

An Fadi Illolin Shigar Amurka Yaki da Boko Haram da Sauran 'Yan Ta'adda

  • Kungiyar PeacePro ta yi Allah-wadai da shirin Amurka na kai hare-haren jiragen yaki kan ‘yan ta’adda a Afrika
  • Kungiyar ta ce irin wadannan hare-hare kan haddasa karin rikici maimakon kawo karshen matsalar tsaro.
  • PeacePro ta bukaci kasashen Afrika su dauki matakan tsaro na cikin gida ba tare da dogaro da kasashen waje ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar PeacePro ta bayyana matsayarta kan batun hare-haren jiragen yaki da Amurka ke shirin kaiwa kan ‘yan ta’adda a nahiyar Afrika.

Kungiyar ta bayyana cewa tarihi ya nuna cewa hare-haren kasashen waje kan kara ta’azzarar matsalar tsaro maimakon kawo karshenta.

jirgin soji
An nuna shakku kan shigowar sojin Amurka Afrika. Hoto: Nigeria Air Force HQ
Asali: Getty Images

Vanguard ta rahoto cewa shugaban kungiyar PeacePro, Abdulrazaq Hamzat ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Kara karanta wannan

"Ba abin da za a fasa," USAID ta fadi halin da tallafawa Najeriya ke ciki duk da zarge zarge

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani taro da aka gudanar a Zambia, babban kwamandan rundunar sojin saman Amurka a Afrika, Janar James Hecker, ya ce za su ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a Afrika.

PeacePro ta yi Allah-wadai da matakin Amurka

Shugaban kungiyar PeacePro, Abdulrazaq Hamzat, ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana rashin amincewar su da wannan yunkuri na Amurka.

A cewarsa, nahiyar Afrika na bukatar hanyoyin magance matsalar tsaro da kasashen yankin za su jagoranta da kansu ba tare da tsoma bakin kasashen waje ba.

Hamzat ya ce:

"Yayin da muke fahimtar cewa Afrika na fama da matsalolin tsaro, muna tsayin daka kan matsayar cewa ba hare-haren kasashen waje ne mafita ba.
Hare-haren da Amurka ta yi a baya a kasashe irin su Libya da Somaliya ba su kawo karshen matsalar tsaro ba, sai dai kara ruruta wutar rikici."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun bankaɗo jihar da fitinannen ɗan ta'adda ya fake a Arewa

Illolin hare-hare daga kasashen waje

A cewar PeacePro, tarihi ya nuna cewa duk lokacin da aka kai irin wadannan hare-hare a Afrika, yakan haddasa karin matsaloli maimakon samar da mafita.

Hamzat ya kawo misali da hare-haren NATO da Amurka suka kai a Libya wanda ya kawo karshen mulkin Muammar Gaddafi amma kuma ya jefa kasar cikin rudani da rikici.

Haka zalika, duk da hare-haren da Amurka ke kaiwa a Somaliya, kungiyar Al-Shabaab har yanzu tana ci gaba da kai hare-hare.

Ya ce kasancewar sojojin a kasashen Sahel bai hana yaduwar ta’addanci ba, sai dai ya janyo karin adawa da kasashen yamma wanda ya haifar da juyin mulki a Mali, Burkina Faso da Nijar.

Trump
Shugaban Amurka yayin wani taro. Hoto: Donald J. Trump
Asali: Getty Images

Hanyoyin magance matsalar tsaro

Kungiyar PeacePro ta ce mafi dacewa shine kasashen Afrika su kirkiro hanyoyin magance matsalar tsaro da kansu maimakon dogaro da kasashen waje.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyyar PDP zai shafi takarar Atiku a zaben 2027? NYFA ta magantu

Daga cikin hanyoyin da kungiyar ke bukatar a dauka sun hada da karfafa hukumar Tarayyar Afrika (AU) da ECOWAS domin su jagoranci yaki da ta’addanci.

Hakazalika, kungiyar ta bukaci a mayar da hankali kan:

  • Karfafa cibiyoyin leken asiri a kasashen Afrika domin hana hare-haren ta’addanci tun kafin su faru
  • Inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Afrika don yakar ‘yan ta’adda
  • Magance tushen matsalolin tsaro kamar fatara, rashin adalcin siyasa da kuma tsattsauran ra’ayi

Gargadi ga kasashen Afrika

Hamzat ya gargadi gwamnatocin Afrika da su guji bai wa kasashen waje damar amfani da kasashen su a matsayin matattarar hare-haren soja.

Ya ce:

"Kasancewar dakarun kasashen waje a Afrika na rage ikon da kasashen yankin ke da shi wajen tafiyar da tsaro.
"Idan har ba mu farka ba, za mu kasance filin gwaji da yaki na kasashen waje har abada."

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka za su faraa kai zafafan hare hare kan Boko Haram

A karshe, PeacePro ta bukaci gwamnatin Najeriya da sauran kasashen Afrika da su fifita hanyoyin diflomasiyya da hadin gwiwar tattalin arziki wajen shawo kan matsalar tsaro.

Ta kuma bukaci Amurka da ta canza salon siyasar ta a Afrika ta hanyar bunkasa tattalin arziki da bayar da tallafin tattalin basira maimakon amfani da karfin soja.

Sojoji sun ceto mutane a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun yi rubdugu kan 'yan ta'adda a wasu yankuna na jihar Neja.

Farmakin ya hada da dakarun soji, 'yan sanda da 'yan banga inda aka samu nasarar ceto mutane kusan 50 da dabbobi da dama wajen 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng