El Rufai Ya Fadi Abin da Mutane ba Su Sani ba game da Atiku a Mulkin Obasanjo
- Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yabawa Atiku Abubakar a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo
- El-Rufai ya ce Atiku ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki a lokacin mulkin daga 1999 zuwa 2007
- A cewarsa, Atiku ne ya jagoranci shirye-shiryen sayar da kadarorin gwamnati, inda El-Rufai ya rike shugabancin BPE, wanda ke karkashin ofishinsa
- Duk da cewa El-Rufai ya soki Atiku a 2016, yanzu ya ce ba a yaba masa kan manufofin tattalin arziki ba, saboda mutane suna mantuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya kwarara yabo ga tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar.
Tsohon gwamnan ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo gyare-gyaren tattalin arziki a zamanin Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan
"Najeriya ta yi rashi": Atiku da Malam El Rufai sun sake haɗuwa, bidiyo ya bayyana

Asali: Twitter
Atiku da El-Rufai sun hadu wurin ta'aziyya
TheCable ta ce El-Rufai ya fadi haka ne yayin ziyarar ta'aziyya ga iyalan Edwin Clark inda ya ce Atiku ya taka rawar gani wajen tsara manufofin tattalin arziki a lokacin Obasanjo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan haduwar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya shiga tawagar Atiku Abubakar, sun je ta'aziyya gidan marigayi Edwin Clark.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce sun yi wa marigayin adddu'ar samun salama tare da bai wa iyalansa haƙurin rashin da suka yi.
A nasa jawabin, Malam Nasiru El-Rufai ya yabawa Atiku bisa yadda ya jagoranci tsare-tsaren bunƙasa tattalin arziki a mulkin Obasanjo.

Abin da El-Rufai ya ce game da Atiku
Atiku ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa a lokacin wato Obasanjo daga 1999 zuwa 2007, cewar Vanguard.
Haka kuma, shi ne ke kula da sayar da kadarorin gwamnati, tare da ofishin BPE da El-Rufai ke jagoranta a lokacin.
“Kowa ya kasa yaba wa Alhaji Atiku Abubakar kan tsara manufofin tattalin arziki a mulkin Obasanjo.
"Da yawa daga abin da muka yi, mun yi ne a ƙarƙashin jagorancinsa lokacin yana mataimakin shugaban kasa.
“Wataƙila saboda ba ma rubuta hakan, kuma mutane ba sa karanta tarihi, muna yawan mantawa.
"Mun fi tuna abubuwa marasa kyau kawai, Wataƙila haka ɗabi'ar ɗan adam take.”
- Nasir El-Rufai
A 2016, Nasir El-Rufai ya caccaki Atiku a lokuta da dama yana zarginsa da kwarewa wajen yada karya.
Masana sun ce El-Rufai na ruguza siyasarsa
Mun kawo muku labarin cewa masana sun bayyana rigimar da Nasir El-Rufai ke yi da Gwamna Uba Sani, APC, da NSA Nuhu Ribadu ka iya lalata masa siyasa a nan gaba.
Masanin siyasa, Kelly Agaba, ya ce hakan na iya shafar siyasar El-Rufai a 2027 duba da shirin haɗaka da yake yi da wasu daga cikin jagororin jam'iyyun adawa.
Agaba ya ce sukar El-Rufai ga jagorancin APC da matsalolinsa da Uba Sani da Ribadu na iya nisantar da shi daga manyan jiga-jigai a jam’iyyar.
Asali: Legit.ng