Yan Bindiga Sun Kutsa da Karfin Tsiya cikin Gida, Sun Sace Malaman Addini 2 a Adamawa

Yan Bindiga Sun Kutsa da Karfin Tsiya cikin Gida, Sun Sace Malaman Addini 2 a Adamawa

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu mahara sun sace fastoci biyu, Rabaran Mathew David Dusami da Rabaran Fr. Abraham Samman.
  • Maharan sun dace Fasto Samman na Jalingo da Fasto Dusami na Yola a Gwaida Malam, Numan da ke jihar Adamawa
  • 'Yan bindigar sun kutsa gidan fastocin da safiyar Asabar 22 ga watan Fabrairun 2025 dauke da makamai, suka kwashe su
  • Kwamishinan 'yan sanda, CP Dankombo Morris, ya bukaci jama’a su taimaka da bayanai, yana mai cewa doka za ta hukunta masu hannu a sacewar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Mahara sun sace fastoci biyu, Rabaran Mathew David Dusami na cocin Katolika a Yola da Fasto Abraham Samman na Jalingo.

Kwamishinan ‘yan sanda na Adamawa, CP Dankombo Morris, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai Allah wadai da satar fastocin.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun hadu sun gwabza artabu da 'yan bindiga

Yan bindiga sun sace malaman addini 2 a Adamawa
Yan bindiga sun yi ta'asa a Adamawa, sun dauke malaman coci 2. Hoto: Legit.
Asali: Original

Tashin bindiga ya raunata masu ibada a Adamawa

Morris ya ce an sace fastocin ne a gidan daya daga cikinsu da ke Gwaida Malam a karamar hukumar Numan da safiyar Asabar, cewar Leadership..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hari na zuwa ne kwanaki uku bayan wani mafarauci ya harba bindiga ba da gangan ba yayin taron cocin LCCN a Demsa da ke jihar Adamawa a Arewacin Najeriya.

Lamarin da ya faru ya yi sanadin raunata akalla mutane takwas yayin da aka kai su asibiti suna karbar kulawa domin tabbatar da ba su kulawa.

Yan sanda sun kama mafaraucin yayin da Kwamishinan ‘yan sanda ya gargadi masu tsaron irin haka kan daukar bindiga wurin taruka.

Bindigar mafarauci ta tashi bisa kuskure

An sace malaman coci 2 a Adamawa

Kwamishina, Morris ya ce an sace fastocin ne a gidan daya daga cikinsu da ke Gwaida Malam a karamar hukumar Numan da safiyar Asabar, cewar Leadership..

‘Yan bindigar dauke da makamai sun kai farmaki misalin karfe hudu na safe, suka dauke su zuwa inda ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sanar da fara daukan 'yan sanda a karon farko a 2025

Morris ya ce rundunar ‘yan sanda ta tura jami’ai da kayan aiki don bin sawun ‘yan bindigar da ceto fastocin ba tare da wani rauni ba.

Ya ce kokarin rundunar zai tabbatar da kama masu hannu a sacewar tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Morris ya jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da hana aikata laifuka a jihar.

"An sace shugabannin addini da ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda ke kokarin wanzar da zaman lafiya."

- In ji CP Morris

Ya bukaci jama’a su kwantar da hankulansu, tare da ba ‘yan sanda goyon baya da bayanai don kubutar da fastocin da kuma kama masu laifi.

Yan bindiga sun sace bayin Allah a asibiti

Mun ba ku labarin cewa Rundunar 'yan sandan Adamawa ta tabbatar da cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace akalla mutane hudu a jihar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da kai harin da aka kai asibitin koyarwa na Maodibbo.

Nguroje ya kuma cewa a halin da ake ciki an aika dakaru har kashi biyu domin bin sahun 'yan bindigar da suka doshi iyakar Najeriya da Kamaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.