Rai Ya Yi Halinsa: Tsohon Sanatan Bauchi Ya Rasu a Abuja, an Shirya Jana'izarsa
- Tsohon sanatan Bauchi ta Kudu, Lawal Yahaya Gumau, ya rasu a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.
- Sanata Gumau ya rasu ne da misalin karfe 3:45 na daren yau Asabar 22 ga watan Faburairun 2025 yana da shekaru 57 a duniya
- Gumau ya fara zama sanata a 2018 bayan mutuwar Ali Wakili inda aka sake zabensa a 2019, amma bai yi nasara a 2023 ba
- Marigayin ya taba zama dan majalisa daga 2011 zuwa 2018, ana sa ran za a yi jana’izarsa a Abuja ranar Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Tsohon dan majalisar da ya wakilci Bauchi ta Kudu, Sanata Lawal Yahaya Gumau, ya rasu da dare a Abuja.
Sanata Gumau ya rasu bayan ya sha fama da gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 57 a duniya a daren yau Asabar 22 ga watan Faburairun 2025.

Asali: Facebook
Sanata Gumau ya bar jam'iyyar NNPP kafin rasuwarsa
Mutuwar tsohon sanatan ta tabbata ne ta hannun tsohon hadiminsa, Comrade Haruna Usman Muhammad, yayin wata hira da wakilin Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan zaben 2023, Sanata Lawal Yahaya Gumau ya sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP bayan yasha kaye a zaɓe.
An ce sanatan ya tattara ƴan komatsansa ya koma jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Bauchi inda ta kasance mai adawa a Najeriya.
Sanatan ya koma bayan gwamnan jihar Bauchi inda ya buƙaci duk magoya bayan sa da su yi masa ruwan ƙuri'u a zaɓe mai zuwa.
Sauye-sauyen sheka da marigayin ya yi
An ce Sanata Gumau ya fara wakiltar yankinsa a 2018 bayan lashe zaben cike-gurbi da aka yi bayan mutuwar Sanata Ali Wakili.
An sake zabensa a babban zaben 2019, inda ya ci gaba da wakiltar yankin har zuwa 2023.
Sai dai duk kokarinsa na komawa majalisar dattawa a zaben 2023 bai yi nasara ba wanda ya rasa damar shiga majalisa.

Kara karanta wannan
Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci

Yaushe za a sallar jana'izar Sanata Gumau?
Kafin ya zama sanata, ya shafe shekaru bakwai a majalisar wakilai, yana wakiltar mazabar Toro daga 2011 zuwa 2018.
Marigayin ya shahara wajen kokarin samar da dokoki, ayyukan raya kasa, da tallafawa matasa a yankinsa.
An samu labarin cewa za a yi jana’izar tsohon dan majalisar a ranar Asabar 22 ga watan Faburairun 2025 a Abuja.
Al'umma da dama sun yi jimamin rasuwar marigayin inda suka kwatanta shi da mutumin kirki.
Kungiya ta taso sanatan Bauchi a gaba
A baya, mun ba ku labarin cewa An fara taso sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa, Shehu Buba Umar, a gaba kan rashin taɓuka abin kirki.
Wata ƙungiyar siyasa ta yi barazanar yi wa sanatan kiranye saboda gaza cika alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe inda suka caccaki salon shugabancinsa.
Ƙungiyar ta ba shi wa'adin sati ɗaya kan ya gyara siyarsa ko kuma ta ci gaba da shirinta na ganin ya dawo gida daga majalisa tare da zaben wanda zai tabuka musu wani abu.
Asali: Legit.ng