Zargin tallafawa Boko Haram: Tsohon Shugaban Kiristoci, CAN Ya Fadi Abin da Ya Sani
- Tsohon shugaban Kiristocin Najeriya, CAN, Samson Ayokunle, ya ce bayyanar da zargin cewa USAID na daukar nauyin Boko Haram ya zo a makare
- Ayokunle ya ce tun da dadewa CAN ta gano akwai masu daukar nauyin 'yan ta'adda, amma gwamnati ba ta dauki matakin bincike da dakatarwa ba
- Hakan ya sa majalisa ta kira shugabannin tsaro don bayani kan zargin yayin da jakadan Amurka ya musanta cewa USAID na daukar nauyin Boko Haram
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Fasto Samson Ayokunle ya yi magana kan daukar nauyin Boko Haram.
Ayokunle ya ce zargin da dan majalisar Amurka, Scott Perry ya yi cewa USAID na daukar nauyin 'yan ta'adda, ciki har da Boko Haram, ya zo a makare.

Kara karanta wannan
"Ba abin da za a fasa," USAID ta fadi halin da tallafawa Najeriya ke ciki duk da zarge zarge

Asali: Facebook
An zargi kasashen ketare da hannu a Boko Haram
Tsohon shugaban kungiyar ya bayyana haka ne a cikin shirin 'Inside Sources' da Channels TV ke watsa wa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tun farkon fara ta'addancin Boko Haram yake zargin kasashen ketare suna da hannu a lamarin.
“Ina zargin kasashen waje, musamman Majalisar Dokokin Amurka, idan da gaske sun san wannan gaskiya tun da dadewa, me ya sa yanzu suka fito da ita? Ba makare suke ba? Me yasa aka bari aka yi wa Najeriya haka?"
"Mun riga mun yi shakku tun da dadewa, saboda lokacin da shugaba (Goodluck) Jonathan ke rokon Amurka, sun ki amincewa.
"A lokacin shugaba (Barack) Obama, suna cewa sojojinmu ba za su yi taka-tsantsan da makamai ba.”
- Cewar Ayokunle

USAID: An bukaci gwamnati ta dauki mataki
Ayokunle ya ce CAN ta dade tana gargadin cewa akwai masu daukar nauyin 'yan ta'adda da kuma isar da kudade da makamai gare su, amma ba a saurare ta ba.

Kara karanta wannan
Dan Majalisa ya fallasa inda Bello Turji yake, an zargi ya ƙaƙaba N25m ga yan kauye
Ya ce sai yanzu aka fara jin gaskiya, ana zargin USAID da daukar nauyin Boko Haram a Najeriya.
Tsohon shugaban CAN ya ce kada a yi watsi da zargin dan majalisar Amurka saboda ba zai wasa da wannan lamari ba.
Ayokunle ya soki hukumomin tsaro, yana cewa sun kasa gano tushen kudaden 'yan ta'adda har sai da dan majalisar Amurka ya fallasa lamarin.
Ayokunle ya kara da cewa:
“Ba zan dauki Scott Perry da wasa ba, domin bai ambaci Najeriya kadai ba; ya ce ana amfani da USAID haka a Pakistan, Afghanistan, da wasu wurare."
"Shin zai yi irin wannan batu ba tare da wata hujja ba? Ba za a dauki irin mutumin nan da wasa ba. Me zai sa ya zargi wata hukuma daga kasarsa?”
Boko Haram: Majalisa ta gayyaci Ribadu, DSS
Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro na NIA da DIA su bayyana a gare ta kan zargin cewa USAID tana ba Boko Haram kudin tallafi.

Kara karanta wannan
Amurka ta yi baki biyu, ta musanta zargin dan majalisa kan daukar nauyin Boko Haram
Daga cikinsu akwai Mallam Nuhu Ribadu da sauran shugabannin hukumomin DSS da NIA da DIA bayan bukatar bincike daga Sanata Ali Ndume.
Sanatoci sun nuna damuwa kan wani bidiyo da ke nuna wani dan majalisar Amurka, Scott Perry, yana zargin USAID da daukar nauyin ayyukan ta’addanci.
Asali: Legit.ng