"Ba Abin da Za a Fasa," USAID Ta Fadi Halin da Tallafawa Najeriya ke Ciki Duk da Zarge Zarge

"Ba Abin da Za a Fasa," USAID Ta Fadi Halin da Tallafawa Najeriya ke Ciki Duk da Zarge Zarge

  • Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya tabbatar da cewa Amurka za ta ci gaba da bayar da tallafi ga kasashen da ke bukatar hakan
  • Sakataren ya bayyana cewa akwai wasu shirye-shiryen da ba su dace su ci gaba da wanzuwa ba kuma ana ci gaba da binciken wasu daga cikin tsare-tsaren
  • A baya-bayan nan dai, wani dan majalisar Amurka, Scott Perry ya yamutsa hazo da wani zargi a kan hukumar ba da tallafi ga kasashen waje ta USAID
  • Mista Perry ya ce akwai hannun hukumar kasarsa wajen ingiza rikice-rikicen ta'addanci a sassa daban-daban, ciki har da Boko Haram a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Amurka - Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa Amurka ta ci gaba da bayar da tallafi na ƙetare duk da dakatar da shirye-shiryen Hukumar Tallafin Ci gaban Ƙetare ta Amurka (USAID).

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na kara karfi, sun kai hari kan jami'an tsaro inda ake zargin Turji ya boye

Wannan na zuwa ne bayan zargin da ake na cewa da akwai hannun hukumar USAID dumu-dumu a cikin daukar nauyin ta'addanci a sassan duniya, har da Najeriya.

Marco
Amurka na ci gaba da ba Najeriya tallafi Hoto: Marco Rubio
Asali: Facebook

Zagazola makama ya wallafa a shafin X cewa Rubio ya sake tabbatar da kudurin gwamnatin Amurka na bayar da tallafi na ƙetare, amma ya kare duba ayyukan USAID.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka za ta ci gaba da raba tallafi

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa ba sa adawa da ba da tallafi ga kasashen da ke da bukatar hakan.

Marco
Marco ya ce akwai shirye-shiryen Amurka da aka dakatar Hoto: Marco Rubio
Asali: Facebook

Ya ce:

“Ba na adawa da tallafin ga kasashen ƙetare. Na goyi bayan tallafi ga kasashen ƙetare.
"Zamu ci gaba da bayar da tallafi. Babu wanda ya ce zamu ki ba da tallafi."

Dakatar da shirye-shiryen da ke samun tallafi daga USAID ya biyo bayan wani sabon tsarin gyaran aiki a cikin hukumar, wanda aka fara a zaman shugabancin Shugaba Donald Trump.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun bankaɗo jihar da fitinannen ɗan ta'adda ya fake a Arewa

Amurka ta dakatar da wasu shirye-shirye

A wani bangaren, Elon Musk, wanda ke shugabantar sabon reshen da aka kafa na Department of Government Efficiency (DOGE), ya soki USAID, yana mai cewa akwai bukatar a wargaza ta.

Bayan dakatar da shirye-shiryen, ma’aikatan USAID a duniya sun rasa aiki, kuma an cire rahotannin kudi da wani bangaren bayanan hukumar daga shafin yanar gizon hukumar.

Amurka ta musanta hannun USAID a Boko Haram

A wani labarin, mun ruwaito cewa Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya musanta zargin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Duniya ta Amurka (USAID) na daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Mills ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja, bayan gabatar da jawabi a taron Gwamnonin Najeriya (NGF) a daren Laraba, a daidai lokacin da ake zargin USAID da hura rikici.

Mills ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da zargin cewa USAID tana taimakawa Boko Haram a Najeriya, musamman ganin yadda kasar take taimaka wa Najeriya wajen yaki da Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel