Obi Ya Fadi Yadda Salon Mulkin IBB Ya Saɓa da Sauran Shugabannin Najeriya
- Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya ce Janar Ibrahim Babangida ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya
- Obi ya yaba wa IBB bisa rubuta littafinsa, yana mai cewa jama'a za su koyi abubuwa da dama daga cikin littafin da aka wallafa
- Tsohon dan takarar ya yaba wa Babangida bisa amincewa da nasarar MKO Abiola a zaben 1993, wanda zai hada kan jama'ar kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya yaba wa tsohon Shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida bayan kaddamar da littafinsa Abuja.
Tsohon gwamnan ya halarci taron kaddamar da littafin tare da manyan 'yan siyasa, ciki har da Shugaban ƙasa Bola Tinubu, tsoffin shugabannin ƙasa da suka halarci taron.

Asali: Twitter
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X game da kaddamar da littafin ranar Alhamis a Abuja, Obi ya ce ba za a iya misalta gudummawar Babangida ga tattalin arzikin Najeriya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'IBB ya jijjaga tattalin arziki' - Obi
A cewarsa, Najeriya ta shaida ci gaba mai yawa, musamman a sashen kudi, a ƙarƙashin shugabancin tsohon shugaban ƙasar.
Ya ce:
“Gudummawar IBB ga tattalin arzikin Najeriya da goyon bayansa mai ƙarfi ga ci gaban kasuwanci da kuma haɓaka sashen masu zaman kansu ba za a iya auna su ba.”
“A ƙarƙashin shugabancinsa, Najeriya ta shaida ci gaba mai yawa, musamman a cikin sashen kudi.
"Ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta Najeriya mai haɗin kai da adalci, da kuma yanayin tattalin arzikin, yana tabbatar da manufofi da suka ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ci gaban tattalin arziki.”
Peter Obi ya jinjinawa IBB
Obi ya kuma jinjinawa Babangida bisa rubuta littafin, yana mai cewa rubuta tarihin abubuwan da ya fuskanta a lokacin da yake mulki zai bai wa ‘yan Najeriya damar daukar darussa.

Asali: Twitter
Ya ce:
“Rubuta irin wannan tarihin yana da kyau, domin yana ba mu damar koyon abubuwa daga waɗanda suka yi hidima kuma suka bar babban tasiri a kasar.
"Ina fatan karanta wannan littafi, wanda ba shakka yana ɗauke da darussa masu kyau.”
1993: Obi ya ji dadin bayyana shugaban kasa
Peter Obi ya ji dadin yadda gaskiya ta fito a kan zaben 1993, wanda aka rika bayyana wa a matsayin daya daga cikin zabukan Najeriya mafi inganci.
IBB ya amince cewa Chief MKO Abiola ne ya lashe zaben 12 ga watan Yuni, 1993, yana mai cewa wannan amincewa hanya ce da za ta tabbatar da hadin kan kasa.
Manyan Najeriya sun halarci taron IBB
A wani labarin, mun wallafa cewa shugabannin Najeriya, ciki har da Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo, sun taru a Abuja don girmama tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida.
An kaddamar da littafin a ranar 20 ga Fabrairu, 2025, a dakin taro na otel din Transcorp Hilton a Abuja, inda ya bayyana abubuwa da yawa, ciki har da wanda ya ci zaben 1993.
Asali: Legit.ng