Bayan Saukar Farashi, an Kawo Tallafin Abinci na Dala Miliyan 1 jihohin Arewa

Bayan Saukar Farashi, an Kawo Tallafin Abinci na Dala Miliyan 1 jihohin Arewa

  • Bankin Raya Afirka (AfDB) ya bayar da tallafin Dala miliyan 1 domin rage yunwa a wasu jihohin Arewacin Najeriya
  • Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) tana aiki da gwamnatin Najeriya don taimaka wa al'ummomin da ambaliya ta shafa
  • Rahotanni na hasashen cewa mutane miliyan 33 ka iya fuskantar matsalar rashin abinci nan da watan Agusta shekarar 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Bankin Raya Afirka (AfDB) ya ba da tallafin dala miliyan 1 daga asusun taimakon gaggawa domin rage matsalar yunwa a yankunan da ambaliya ta shafa a Arewa maso Gabas.

Tallafin na cikin haɗin gwiwa da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) don taimakawa wadanda ke fama da matsalolin da tashin hankula, talauci da ambaliya suka haifar.

Kara karanta wannan

Yadda jiga jigan Najeriya suka tara Naira Biliyan 17 ga IBB a zama 1

Tallafin AFDB
AfDB ya tallafawa wasu jihohin Arewa da kudi domin sayen abinci. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Darektan hukumar WFP a Najeriya, David Stevenson, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Maiduguri, kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar yunwa a Arewa maso Gabas

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar da ta faru a watan Satumba 2024 a jihar Borno ta raba dubban mutane da muhallansu, lamarin da ya kara tsananta matsalar rashin abinci a yankin.

David Stevenson ya ce da dama daga cikin mutanen da suka fara gyara rayuwarsu bayan shekaru da dama na tashin hankali, yanzu sun sake fadawa cikin mawuyacin hali sakamakon ambaliyar.

A cewarsa, AfDB ta bayar da tallafin ne domin rage wahalar da wadannan mutane ke fuskanta, musamman duba da hauhawar farashin abinci da kuma halin da tattalin arziki ke ciki.

Rahoton Cadre Harmonisé da ake fitarwa sau biyu a shekara domin kimanta matsalar rashin abinci a jihohi 26 da Abuja, ya nuna cewa mutane miliyan 33 a Najeriya na iya fuskantar yunwa daga nan zuwa watan Agusta 2025.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya fallasa inda Bello Turji yake, an zargi ya ƙaƙaba N25m ga yan kauye

Ambaliya
Yadda aka yi ambaliyar ruwa a a Borno. Hoto: Muhammad Kime
Asali: Facebook

AfDB ta yabawa gwamnatin Najeriya

Shugaban AfDB a Najeriya, Abdul Kamara, ya jinjinawa kokarin da gwamnatin tarayya da hukumar WFP ke yi domin tallafa wa al’umma a irin wannan mawuyacin hali.

A cewarsa:

"Wannan tallafi na AfDB wani bangare ne na kokarin bankin na ci gaba da sake fasalin shirin raya aikin gona da daidaita sauyin yanayi (PIDACC),
"Shiri ne da ke bai wa mutane tallafin inganta rayuwa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa."

Kamara ya kuma bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka matuka wajen rage radadin wahalar da al'ummomi ke fuskanta, musamman a yankunan da rikice-rikicen 'yan ta'adda suka lalata.

A cewarsa, WFP na bai wa mutane sama da miliyan 1 tallafin abinci mai inganta gina jiki a Borno duk wata, wanda ke taimakawa wajen dakile matsalar rashin abinci a jihar.

Matakan rage yunwa da kwanjamewa

Hukumar WFP tana daukar matakai daban-daban domin rage radadin yunwa da cututtukan da ke da nasaba da rashin wadataccen abinci a yankunan da rikici ya yi wa illa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Hukumar na koyar da ma'aikatan lafiya dabarun gano cutar kwanjamewa da kuma yadda za a kula da mata da yara masu fama da matsalar rashin lafiya sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Baya ga haka, WFP na gudanar da shirye-shiryen inganta lafiyar uwa da jariri, wanda ke taimakawa wajen tabbatar da lafiyar iyalai tun daga matakin haihuwa.

Gwamna Radda zai raba abinci a Ramadan

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan 2.3 domin tallafawa al'umma da abinci.

Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa za a tanadi abincin ne domin rabawa talakawa marasa galihu kyauta da kuma sayar wa wasu a farashi mai rahusa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng