'Yan Ta'adda na Kara Karfi, Sun Kai Hari kan Jami'an Tsaro Inda Ake Zargin Turji Ya Boye

'Yan Ta'adda na Kara Karfi, Sun Kai Hari kan Jami'an Tsaro Inda Ake Zargin Turji Ya Boye

  • Jami'an tsaron Sakkwato sun fada tarkon ’yan bindiga bayan sun amsa kiran neman dauki daga mazauna Sabon Birni dake jihar
  • Jami’an tsaron sun bukaci mota daga mahukunta amma ba a basu ba, saboda ba su da izinin aiki ba tare da jami’an tsaro na hukuma ba
  • Bayan sun yanke shawarar isa garin a kan babura ne suka fuskanci an shirya masu kwanton bauna, wanda ya jawo asarar rayuka
  • Hukumar tsaron ta ki cewa komai a kan kisan, sai dai gwamnatin Sakkwato ta tabbatar da lamarin, tare da fadin matakin da aka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sakkwato — ’Yan bindiga sun yi kwanton-bauna tare da kashe jami’an tsaron Sakkwato guda shida a Karamar Hukumar Sabon Birni a ranar Litinin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun bankaɗo jihar da fitinannen ɗan ta'adda ya fake a Arewa

Bayanai sun nuna cewa jami’an sun amsa kiran neman dauki daga mazauna garin da suka hangi ’yan bindiga a yankinsu, amma suka fada tarkon kwanton-bauna da aka shirya musu.

Sokoto
Yan kashe jami'an tsaron Sakkwato Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin yankin ya ce wani abokin aikinsu ne ya sanar dasu shirin wani hari da ’yan bindiga ke kokarin kai wa kusa da Tagirke-Kwatsal, a gefen Unguwan Lalle.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakkwato: ’Yan sa kai sun tafi ceto

Rahotanni sun ce jami’an tsaron sun bukaci a basu motar aiki daga hukumomin karamar hukuma, amma ba a basu ba saboda ba su da izinin gudanar da ayyuka ba tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na hukuma ba.

Bayan gazawar samun mota, sai ’yan sa-kai suka yanke shawarar zuwa kauyen a kan babura, inda suka fada tarkon ’yan bindiga a lokacin da suka isa garin.

Wata majiya ta ce:

"Sun gwabza fada da ’yan ta’adda amma daga karshe an rinjaye su. Maharan sun kashe guda shida daga cikinsu, kuma an gano gawarwakinsu sannan aka binne su a ranar Talata."

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

Abin da mahukunta Sakkwato ke fadi

Kwamandan hukumar tsaron jihar Sakkwato, Kanal Na-Allah Idris (mai ritaya), ya ki cewa komai game da harin da ya yi sanadin rasuwar jami'ansa guda shida.

A gefe guda, mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce bai da masaniya kan harin saboda yana kan aiki a Abuja.

Sai dai, Mai Baiwa Gwamna Ahmed Aliyu Shawara kan Tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya tabbatar da harin, yana mai cewa ana gudanar da bincike don gano cikakken bayani kan lamarin.

Gwamna
Jami'an tsaro sun rasu a Sakkwato Hoto: Office of the SSA new media to the Sokoto State Governor
Asali: Facebook

An gano maboyar fitinannen dan ta'adda

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an tsaron Najeriya sun tabbatar da gano inda wani hatsabibin dan ta'adda, Jan Kare ya fake a jihar Katsina, sai dai ba a san asalin inda yake zaune ba.

Ayyukan ta’addancin Jan Kare hana mazauna jihar sakat, musamman a kananan hukumomin Danmusa, Safana, Dutsin-Ma, Kurfi, da Matazu, inda aka bayyana cewa har haraji yake karba daga jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.