Dan Majalisar Arewa Ya Tayar da Kura kan Mayar da Cibiyar Gwamnati Legas
- Hon. Ahmed Idris Wase ya yi watsi da kudirin mayar da hedkwatar cibiyar FIIRO zuwa yankin Oshodi na jihar Lagos
- Dan majalisar ya ce babu dalilin mayar da hedkwatar cibiyar, duba da cewa Abuja ce cibiyar mulki ta kasa
- A karkashin haka Hon. Wase ya bukaci 'yan majalisa su yi watsi da kudirin tare da yin adalci ga kowane bangaren kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An samu cece-kuce a zauren Majalisar Wakilai yayin da Rt. Hon. Ahmed Idris Wase ya nuna adawarsa ga kudirin da ke neman sauya dokar cibiyar bincike ta FIIRO.
Kudirin da Hon. Fayinka Moses Oluwatoyin ya gabatar yana neman mayar da hedkwatar cibiyar FIIRO zuwa Oshodi, Lagos, tare da kafa wa Shugaban Hukumar wa’adin aiki guda daya kacal.

Asali: Facebook
Hon. Ahmed Idris Wase ya nuna adawa game da kudirin kamar yadda ya wallafa yadda zaman majalisar ya kasance a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin zaman majalisar, Wase ya bayyana cewa tsarin shugabancin Shugaban Majalisa na bai wa kowa dama, kuma yin hakan zai tabbatar da adalci ga kowa da kowa.
Wase ya ce a bar ofishin FIIRO a Abuja
Hon. Ahmed Idris Wase ya bayyana cewa duk lokacin da aka kafa wata hukuma, dole a yi la’akari da tsarin mulkin kasa da kuma inda ya fi dacewa da ita.
Ya ce a da lokacin da aka kafa FIIRO, Lagos ce babban birnin Najeriya, amma tun da aka mayar da babban birnin kasa zuwa Abuja, babu wani dalili da zai sa a koma da ita Lagos.
Hon. Wase ya jaddada cewa kasancewar Abuja ita ce cibiyar mulki ta kasa, hakan yana bai wa kowa damar samun damar shiga da fitar da bayanai daga hukumomin gwamnati cikin sauki.

Kara karanta wannan
'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai
A cewarsa, barin hedkwatar FIIRO a Abuja zai tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya suna da damar cin moriyar ayyukanta ba tare da fifita wani yanki ba.
Kiran Hon. Wase ga majalisa
A jawabinsa, Hon. Wase ya roki ‘yan majalisa su yi fatali da kudirin nan take domin tabbatar da adalci da hadin kan kasa.
Dan majalisar ya ce:
“Ba zai yiwu mu koma mayar da abubuwa baya ba. Hedkwatar FIIRO ta kasance a Abuja, kuma dole ne ta ci gaba da kasancewa nan.”
Ya yi kira ga Hon.Oluwatoyin da ya janye kudirin, tare da tunatar da shi cewa tsarin mulkin kasa yana bukatar sauye-sauyen da za su amfani kowa ba tare da nuna bambanci ba.
A cewarsa, yunkurin mayar da hedkwatar cibiyar zuwa Lagos tamkar fifita wani yanki ne a kan sauran yankuna na Najeriya.
Hon. Wase ya bukaci dakile kudirin
A karshe, Wase ya bukaci ‘yan majalisa su ki amincewa da kudirin, yana mai cewa lallai ya kamata a dakile shi.
Ya bayyana cewa idan aka amince da wannan sauyi, zai iya haifar da matsala a nan gaba, inda za a rika daukar matakai ba tare da la’akari da bukatun kasa gaba daya ba.
Hon. Wase ya jagoranci bude masallaci
A wani rahoton, kun ji cewa Hon. Wase ya jagoranci tagawa domin bude sabon masallacin juma'a a jihar Filato.
Legit ta rahoto cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ne ya sabunta masallacin kuma ya dura jihar Filato domin bude shi.
Asali: Legit.ng