Ginin Makaranta Ya Rufta Kan Ɗalibai Suna Tsakiyar Karatu a Yobe, An Rasa Rai

Ginin Makaranta Ya Rufta Kan Ɗalibai Suna Tsakiyar Karatu a Yobe, An Rasa Rai

  • Wata daliba ta rasu, yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon rushewar bangon ajin su a makarantar GGSS Potiskum, jihar Yobe
  • Lamarin ya faru da misalin karfe 12:30 na rana, lokacin da daliban ke karatu, ba tare da wani malami a cikin ajin da ya rushe ba
  • Gwamnatin jihar Yobe ta ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin ruftawar ginin tare tare da daukar matakan kariya don gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yobe - Wata daliba ta rasu, yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon rushewar bangon aji a makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Potiskum, jihar Yobe.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na rana, lokacin da daliban ke cikin ajinsu.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyyar PDP zai shafi takarar Atiku a zaben 2027? NYFA ta magantu

Gwamnatin Yobe ta magantu da gini ya rufta kan dalibai suna tsaka da karatu
Gini ya rufta kan dalibai suna tsaka da karatu a jihar Yobe. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Ginin makaranta ya rufta kan daliban Yobe

Jaridar Daily Trust, ta rahoto majiyar tana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A lokacin da wannan mummunan lamari ya faru, mafi yawan dalibai suna daukar darasi a makaranta. Ba a sami wani malami a ajin da lamarin ya shafa ba."

An tabbatar da mutuwar wata daliba daga karamar hukumar Fika, yayin da wasu dalibai biyar suka samu raunuka kuma ana basu kulawa a asibiti.

An gano sunayen daliban da suka jikkata su ne: Fatima Bala Adamu, wacce har yanzu ba ta farfado ba, sai kuma Fatima Abba Idris.

Sauran daliban da abin ya shafa sune: Hafsat Ahmed, Fatima Ibrahim, da Hafsat Abubakar Maina, wadanda ke samun kulawa a asibiti.

Gwamnatin Yobe ta fadi halin da daliban ke ciki

Jami'an gwamnatin Yobe na duba ginin ajin da ya rufta kan dalibai
Jami'an gwamnatin Yobe na duba ginin ajin da ya rufta kan dalibai. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Gwamnati ta tabbatar da faruwar lamarin, inda babban sakataren ma'aikatar ilimi ta jihar Yobe, Dr. Bukar Aji Bukar, ya bayyana cewa lamarin ya shafi ajujuwa biyu masu dauke da dalibai 50.

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

"Akwai dalibai kusan 25 a kowane aji. Yayin da suke cikin darasi, wani bangare na ginin ajin ya rushe, inda ya jikkata dalibai biyar," inji sakataren.

Jaridar Vanguard ta rahoto Dakta Bukar ya kara da cewa:

"Daya daga cikin daliban ta mutu a hanyarsu ta zuwa asibiti, sauran kuma suna samun kulawa. Mun ziyarce su, kuma suna cikin mauyacin hali."

An nuna muhimmancin kula da gine-ginen makaranta

Babban sakataren ya ce suna jiran rahoto daga makarantar, domin sanar da ma'aikatar gidaje don gano musabbabin rushewar ginin da kuma daukar matakan kariya don hana irin haka a gaba.

Har yanzu ba a fitar da takamaiman matakin da za a dauka ba, amma ana sa ran gwamnati za ta dauki matakan gyara da kariya ga daliban makarantar.

Lamarin ya jawo damuwa sosai a yankin, inda jama’a ke kira ga hukumomi da su dauki matakan gyara gine-ginen makarantu domin kare lafiyar dalibai a gaba.

Kara karanta wannan

Adamawa: An shiga fargaba da bindiga ta tashi a wurin ibada, mutane sun jikkata

Gini ya rufta kan dalibai a Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani gini a makaranta ya rufta kan ɗalibai da ke rubuta jarabawa a Busa Buji, ƙaramar hukumar Jos, jihar Filato.

Rahotanni sun ce iyayen yara sun garzaya wurin neman agaji, yayin da jami’an tsaro suka isa makarantar don dakile matsala.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Jumu’a, 12 ga Yuli, 2024. Ana kokarin ceto ɗaliban da ke cikin baraguzan ginin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.