Bayan Shekaru, DSS Ta Kama Mai Damfara da Sunan Izala da Manyan Malamai
- Shugaban Jibwin na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce an kama wani mutum da ya shafe shekaru yana damfara da sunan Izala
- Rahotanni sun nuna cewa Hukumar DSS ce ta kama wanda ake zargi, Jamilu Abubakar, a Legas bayan Sheikh Bala Lau ya shigar da korafi
- Biyo bayan lamarin, malamin ya ja hankalin al’umma da su guji masu neman taimako da sunan ƙungiyar Izala, musamman a kafafen sada zumunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa wani mutum mai suna Jamilu Abubakar ya shafe shekaru huɗu yana damfara da sunan ƙungiyar.
A cewarsa, masu damfara na amfani da sunan ƙungiyar Izala da na shahararrun malaman ƙungiyar domin yaudarar mutane.

Asali: Facebook
Sheikh Bala Lau ya yi wannan bayani yayin wani taro da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyar JIBWIS ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama mai damfara da sunan Izala
Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa an dade ana kokarin kama wanda ake zargi da wannan damfara amma hakan ya gagara.
Ya ce sun kai ƙorafi ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, amma ba a samu nasarar kama wanda ake zargi ba har sai da ya yi magana da sabon shugaban hukumar DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi.
A cewarsa, bayan tattaunawa da shugaban DSS, sai aka bai wa jami’an tsaro mako guda domin kamo wanda ake zargin.
“Yanzu haka an kama shi a Legas, sunansa Jamilu Abubakar. Ya shafe shekara huɗu yana damfara da sunan Izala,”
- Sheikh Bala Lau
Ya ce wanda ake zargi zai gurfana a kotu a Legas, kuma dole ne ya mayar da duk kuɗin da ya karɓa daga hannun mutane ko kuma a yanke masa hukunci.
Jinjina ga DSS da gargaɗi ga al’umma
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jinjinawa shugaban DSS bisa wannan ƙoƙari da ya yi na tabbatar da an kama wanda ake zargi.
Malamin ya ce:
“Na kira sabon shugaban DSS, sai ya ce min na ba shi mako guda. A yanzu ga shi an kama wanda yake damfara da sunan Izala.”
Sheikh Bala Lau ya kuma gargaɗi al’umma, musamman masu amfani da kafafen sadarwa na zamani, da su kula da mutanen da ke neman taimako da sunan ƙungiyar Izala.

Asali: Facebook
Al’umma sun yaba da aikin DSS
Bayan bayyanar wannan labari, jama’a da dama sun nuna jin daɗinsu da yadda jami’an DSS suka kama wanda ake zargi da damfara.
Wasu daga cikin mutanen da suka yi tsokaci sun ce wannan aiki ne da ya dace, kuma hakan zai zama izina ga sauran masu damfara da sunan addini ko ƙungiyoyi.

Kara karanta wannan
Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya
Tun daga hawansa kan mukamin shugaban DSS a ranar 28 ga Agusta, 2024, Adeola Oluwatosin Ajayi ya nuna himma wajen magance laifuffuka irin wannan.
Al’umma na sa ran cewa jami’an tsaro za su ci gaba da gudanar da ayyukansu da kuma hana mutane yin amfani da sunayen addini domin aikata damfara.
Bin Usman zai koma masallacinsa
A wani rahoton, kun ji cewa malaman jihar Kano sun cimma matsaya kan sabanin da aka samu a masallacin Jami'urrahma da Sheikh Bin Usman.
A yanzu haka dai Sheikh Muhammad Bin Usman zai koma limanci a masallacinsa na Sahaba da ke Kundila bayan barin Jami'urrahma.
Asali: Legit.ng