Rigima Ta Barke a Majalisa, Akpabio Ya Fusata bayan Umartar a Yi Waje da Sanata
- Rikici ya barke a majalisar dattawa yayin da aka matsar da kujerar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, amma ta ki amincewa da sabon wurin zama da aka ba ta
- Shugaban majalisa, Sanata Godswill Akpabio, ya samu sanarwa daga Sanata Monguno cewa Natasha na zauna ba bisa ka’ida ba, wanda ya haddasa hayaniya
- Rikicin ya tsananta lokacin da jami’an tsaro suka kewaye Natasha domin fitar da ita daga zauren majalisa bayan gardama mai zafi ta barke
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu hatsaniya a majalisar dattawan Najeriya yayin zamanta.
An samu dan karamin rikici a majalisar yayin da rigima ta barke tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugabancin majalisa kan matsalar wurin zama.

Asali: Facebook
An yi rigima tsakanin Akpabio da Sanata Natasha

Kara karanta wannan
Dan Majalisa ya fallasa inda Bello Turji yake, an zargi ya ƙaƙaba N25m ga yan kauye
Channels TV ta ce matsalar ta fara ne lokacin zaman majalisar tskakonl Sanata Natasha da shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan matsar da kujerar Sanata Natasha yayin zaman majalisa karkashin jagorancin Akpabio, amma ta ki yarda.
Sanata Mohammed Ali Monguno, Shugaban Masu Rinjaye, ya jawo hankalin Shugaban Majalisa kan “zaman da bai dace ba da Sanata Akpoti-Uduaghan ke yi.”
Monguno bai gama bayaninsa ba kafin Natasha ta fara hayaniya, wanda ya sa jami’an tsaro suka kewaye ta domin kokarin fitar da ita daga zauren majalisa.
Monguno ya bayyana cewa dole ne a yi sauye-sauyen don daidaita matsayi bayan wasu ‘yan hamayya sun koma bangaren mafi rinjaye.
Ya ce sauye-sauyen na cikin hurumin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Sanata Natasha ta tubure a majalisar dattawa
Ba tare da ja da baya ba, Sanata Natasha ta daga murya cikin tirjiya, tana fuskantar Shugaban Majalisar Dattawa kai tsaye.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
“Ba na jin tsoron ku. Ko da za a hana ni magana, ba na tsoro. Kun hana ni haƙƙina,”
- In ji Sanata Natasha
Akpabio ya sha alwashin kwace wasu jihohi
A baya, kun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya taɓo batun shirin jam'iyyar APC kan yankin Kudu maso Kudu a zaɓen 2027.
Godswill Akpabio ya bayyana cewa APC ta shirya lashe sauran jihohi huɗu da ba su ƙarƙashin ikonta a zaɓen 2027 mai zuwa.
Akpabio ya bayyana cewa tun da farko ya koma APC ne domin ganin ya jawo mutanen yankin Kudu maso Kudu zuwa cikinta.
Asali: Legit.ng