Dan Majalisa Ya Fallasa inda Bello Turji Yake, an Zargi Ya Ƙaƙaba N25m ga yan Kauye
- Rahotanni sun ce an gano Bello Turji a gabashin Sokoto, inda ake zargin ya kakaba harajin ₦25 miliyan kan wasu kauyuka
- Wani dan majalisar jihar ne, Hon. Aminu Boza ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai
- Hon. Boza ya neman a dauki matakin gaggawa don dakile ayyukan Turji saboda yadda yake cutar da al'umma
- Dan majalisar ya ce Bello Turji yana yankin Isa da Sabon Birni inda ya kakaba harajin miliyoyi ga kowanne kauye
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Wani dan majalisar jihar Sokoto, Hon. Aminu Boza ya fallasa inda rikakken dan ta'adda, Bello Turji yake.
Hon. Boza ya tabbatar da cewa an gano dan bindiga, Bello Turji, a gabashin Sokoto da ke Arewacin Najeriya bayan shan matsin lamba daga rundunar sojojin kasar.

Asali: Original
An ragargaza sansanonin yan ta'adda a Zamfara
Rahoton Zagazola Makama ya ce ana zargin Turji ya kakaba harajin ₦25m kan wasu kauyuka da ke gabashin jihar Sokoto a Arewacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Sojoji sun kai farmaki kan ‘yan bindiga a dazukan jihar Zamfara inda suka ragargaza sansaninsu da ke bayan gari.
Hare-haren sojojin ƙasa da na sama sun taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yammacin kasar.
An kashe hatsabiban yan bindiga kamar Kachalla Na Faranshi tare da mabiyansa a Zurmi, kuma an lalata sansanin Sani Black.
Dan Majalisa ya tona inda Bello Turji yake a Sokoto
An ce dan majalisar dokokin Sokoto, Aminu Boza, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata 18 ga watan Janairun 2025 yana neman a dauki mataki.
“Bello Turji yana yankin Isa da Sabon Birni na Sokoto, Har ya kakaba harajin ₦25 miliyan ga kowanne kauye.
- In ji Aminu Boza
Dan majalisar ya bukaci hukumomin tsaro da shugabannin yankin su kara kaimi wajen yaki da ‘yan bindiga, cewar Sahara Reporters.
Sojoji sun gano maboyar dan ta'adda, Bello Turji
A baya, kun ji cewa Sojojin Operation Fansan Yamma sun samu gagarumar nasara yayin da suka farmaki babbar maboyar Bello Turji a Zamfara.
An ce sojojin sun kai farmakin inda suka gano makamai da harsasai, kuma sun rusa sansanin da Turji ke amfani da shi wajen shirya hare-hare.
Wannan nasara ta kawo cikas ga ayyukan Bello Turji, yayin da sojojin suka kubutar da wasu mata da kananan yara da aka tsare.
Asali: Legit.ng