'Ya Aikata Laifuffuka 5': An Gurfanar da Fitaccen Mawakin Najeriya a Gaban Kotu

'Ya Aikata Laifuffuka 5': An Gurfanar da Fitaccen Mawakin Najeriya a Gaban Kotu

  • Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola Olalomi, wanda aka fi sani da Portable a gaban kotun Abeokuta
  • Portable ya musanta laifuffuka biyar da mai gabatar da karar ke tuhumarsa da su, ciki har da cin zarafi da amfani da makamai
  • An tsare Portable tara bisa tuhumar hadin baki da kai wa jami'an gwamnatin Ogun hari kan yunkurin rufe wata babbar mashayarsa da ke garin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - An gurfanar da shahararren mawaki, Habeeb Okikiola Olalomi, wanda aka fi sani da Portable, a kotun majistare da ke Isabo, Abeokuta, Ogun.

'Yan sun ayyana Portable a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo tun ranar 18 ga Fabrairu bisa zargin cin zarafin jami’an OGPDPA, a jihar Ogun.

Fitaccen mawakin Najeriya, Portable ya gurfana gaban kuliya manta sabo
'Yan sanda sun gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya, Portable a gaban kotu. Hoto: @X_ClusiviTea
Asali: Twitter

An gurfanar da mawaki Portable a kotu

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai

Portable ya mika kansa ga ‘yan sanda a Lagos a ranar Laraba, inda aka miƙa shi ga rundunar Ogun, sannan aka kai shi kotu, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tuhume shi da laifuffuka biyar, ciki har da hadin baki, hari da makamai, da aikata abu mai iya haddasa barna, wadanda duka ya musanta zargin.

Lauyan mawakin, Oluwatoyin Ayodele, ya nemi kotu ta ba shi beli, yana mai cewa Portable ya koyi darasi kuma yana nadama.

Kotu ta ba da belin Portable kan N2m

Mai shari’a O.L. Oke ya ba Portable beli kan Naira miliyan biyu tare da mai tsaya masa da ke da irin wannan adadin.

Rikicin ya fara ne a ranar 5 ga Fabrairu, lokacin da jami’an OGPDPA suka kokarin rufe mashayarsa saboda rashin cika wasu ka'idoji.

Ana zargin Portable da jagorantar wasu 'yan daba a farmakin da suka kai wa jami’an OGPDPA, wanda ya jikkata su kafin su tsere.

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

Portable ya zabgawa malamin addini mari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mawaki Habeeb Olalomi Badmus, wanda aka fi sani da Portable, ya mari wani fasto da ke wa'azi a kusa da shagonsa na sayar da barasa.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a intanet, an ga Portable ya na ikirarin cewa faston na takura wa abokan kasuwancinsa, inda ya gargade shi da ya bar wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.