"Rumbunanmu Fal da Abincin," Najeriya Ta Ƙaryata Fargabar Ƙarancin Hatsi
- Ƙaramin Ministan harkokin noma, Aliyu Abdullahi ya ce Najeriya ba ta fuskantar haɗarin ƙarancin abinci ba
- Ya bayyana haka ne a matsayin martani ga wani rahoto dake bayyana yiwuwar ƴan Najeriya za su samu rashin abinci
- Alhaji Aliyu Abdullahi ya ba da tabbacin matakan da gwamnatin tarayya da na jihohi suke ɗauke din wadata talakawa da abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT Abuja – Karamin Ministan noma, Aliyu Abdullahi ya shawarci ƴan Najeriya a kan su kwantar da hankulansu kan rahoton za a iya samun ƙarancin abinci.
Ya ce Shugaba Bola Tinubu yana sane da muhimmancin tabbatar da an wadata ƙasa da abinci, wanda ya sa ya ayyana dokar ta-baci kimanin watanni biyu bayan kama aiki a kan ɓangaren.

Asali: Getty Images
A hira da yayi da Channels News, Ministan ya jaddada cewa Najeriya ba ta taɓa fuskantar ƙarancin abinci ba, abin da ake fuskanta a yanzu, ba rashin abinci ne ya haddasa shi ba.
Gwamnati ta yi watsi da rahoton ƙarancin abinci
Daily Post ta ruwaito cewa Minista a harkokin noma, Aliyu Abdullahi ya mayar da martani kan labarin da ke bayyana fargabar ƴan Najeriya za su iya fuskantar ƙarancin abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya nanata cewa:
Najeriya ba ta cikin haɗarin ƙarancin abinci; ba ta taɓa kasancewa ba, kuma ba za ta kasance a cikin ƙarancin abinci ba, da ikon Allah.”
“Sai dai ina so in fayyace cewa idan aka ce ƙaranci, yana nufin babu shi kwata-kwata. Najeriya ba ta fuskantar hakan ba, amma akwai matsalolin tattalin arziki da ke tasiri kan wadatar abinci."
"Najeriya ta yi tanadin abinci," Gwamnati
Ministan ya ce, a ƙari ga manyan rumbunan ajiya da gwamnatin tarayya ke kula da su, wasu jihohi da dama sun rungumi dabarar ajiyar abinci domin ƙarfafa wadatar abinci a ƙasar. Ministan ya musanta zargin da ke cewa Najeriya ba ta wadatu da abinci ba, yana mai cewa muddin ana iya samun duk nau'in abinci a kasuwa, babu dalilin tada hankalun jama'a.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi kaca kaca da gwamnatin Tinubu, ya tona makircin da APC ke kullawa a Osun
Yunwa: Gwamnati ta kwantar da hankalin ‘yan Najeriya
Abdullahi ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa Shugaba Tinubu yana da niyyar dakile hauhawar farashin abinci da ke ci gaba da samu, tare da daidaita shi yadda kowa zai iya samun abincin da yake so.
Ya ce:
“Mun samu ci gaba sosai wajen samar da shinkafa a kasar nan. Shinkafar da muke nomawa a cikin gida ta isa, sai dai matsalar ita ce da dama daga cikinmu na da sha’awar cin shinkafar da aka shigo da ita daga waje."
Farashin abinci ya sauka
A baya, kun samu labarin cewa a cikin 'yan kwanakin nan, masu saye da sayarwa a shahararriyar kasuwar Singer da ke Kano sun fara jin saukin farashin kayayyakin abinci.
Shugaban kasuwar, Junaidu Zakari ya ce an samu saukin ne bayan ƴan kasuwa sun fara cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na shigo da abinci daga ƙasashen waje a baya-bayan nan.
An kuma bayyana cewa samuwar hatsi daga manoman ƙasar ya ƙara saukaka farashi a kasuwanni, lamarin da ake gani zai wuce azumin watan Ramadana dake karatowa.
Asali: Legit.ng