Saukar Farashi: Gwamna Ya Kawo Shirin Raba Abinci Kyauta a Ramadan

Saukar Farashi: Gwamna Ya Kawo Shirin Raba Abinci Kyauta a Ramadan

  • Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da ware Naira biliyan 2.3 domin sayen hatsi da kayan abinci don tallafawa al'umma a watan Ramadan
  • Kwamishinan Noma na jihar, Farfesa Ahmed Bakori, ya bayyana cewa za a raba kayan ga marasa galihu da kuma sayar da wani bangare da araha
  • Haka zalika, gwamnatin jihar Katsina ta amince da ware Naira biliyan 16.5 domin sayen takin zamani tan 32,000 don tallafawa manoma da saukaka musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki matakin tallafawa al'ummar jihar yayin azumin watan Ramadan da ke tafe.

Bayan taron majalisar zartaswa da gwamna Dikko Umaru Radda ya jagoranta, an amince da ware Naira biliyan 2.3 domin wannan shiri na musamman.

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

Gwamna Radda
Gwamna Radda zai tallafawa al'umma a Ramadan. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamna Dikko Umaru Radda, Ibrahim Kaula Mohammed ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 19 ga Fabrairu, 2025 a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin rabon kayan abinci a Katsina

Kwamishinan Noma da harkokin Dabbobi, Farfesa Ahmed Mohammed Bakori, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar da hatsi da kayan abinci domin rage wa al'umma wahalar azumi.

A cewarsa, za a raba wani bangare kyauta ga dattawa da marasa galihu, yayin da za a sayar da wasu kayan a farashi mai rahusa ga jama'a.

Ya ce wannan shiri wani ci gaba ne daga irin tallafin da aka yi a shekarar da ta gabata, wanda ya taimaka gaya wajen saukaka wahalhalun da ake fuskanta a lokacin azumin watan Ramadan.

Ana fatan shirin zai taimaka wajen kawo sauki ga al'umma yayin da ake cigaba da samun saukin kayan abinci.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Trump zai binciki zargin tallafawa Boko Haram daga Amurka

Radda ya ware N16.5bn kan taki

Baya ga tallafin Ramadan, gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira biliyan 16.5 domin sayen tan 32,000 na takin zamani.

Farfesa Bakori ya bayyana cewa wannan karin taki zai hade da tan 80,000 na takin da ake da shi, wanda zai samar da jimillar buhuna 400,000.

Ya ce ana sa ran fara rabon takin a watan Afrilu domin tabbatar da cewa manoma sun samu taki kafin damina ta fara.

Radda zai ci gaba da rage wahalar jama'a

Gwamnatin Jihar Katsina ta nuna kudirinta na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen rage radadin da jama’a ke fuskanta.

Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin Gwamna Dikko Radda za ta ci gaba da daukar matakai domin inganta jin dadin al'ummar jihar.

Gwamna Radda
Gwamna Radda yayin tallafawa matasa a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

A cewar kwamishinan:

"Wannan shiri wani bangare ne na manufofin gwamnatin jihar na rage radadin tattalin arziki da samar da tallafi ga jama’a, musamman a lokutan bukukuwa da damina.

Kara karanta wannan

Rumbun sauki: Gwamna ya bude wuraren sayar da abinci da araha ga talakawa

Radda ya kafa rumbun sauki

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kafa rumbunan sauki domin karya farashin abinci.

Gwamnatin Katsina ta bayyana tsare tsare da za a bi wajen sayar da abinci ga al'umma a wasu cibiyoyi da aka ware a kananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel