Haduran Tankar Mai: Gwamnatin Tinubu Ta Haramtawa Wasu Tankoki Hawa Titunan Kasar
- Hukumar NMDPRA ta haramta amfani da tankokin mai masu daukar lita fiye da 60,000 a hanyoyin Najeriya
- Rahotanni sun tabbatar cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga Maris din 2025 don rage yawan hadurran hanya
- Hukumar ta yanke wannan shawara ne bayan yawaitar hadurran manyan motocin mai, ciki har da fashewar tanker a Niger da ya kashe mutane 50
- Ana sa ran ba za a sake barin kowace mota mai lodi fiye da lita 60,000 ta ɗauki kaya a kowanne sito ba daga 1 ga Maris, 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta haramta amfani da tankokin mai masu lita fiye da 60,000 a hanyoyin kasar.
Hukumar ta dauki wannan mataki ne domin rage yawan haduran da ake samu da yake sanadin rayuka.

Asali: Original
Yadda aka rasa rayuka sanadin faduwar tankar mai
Da yake magana da ‘yan jarida a Abuja, Daraktan Rarraba Kayayyaki na NMDPRA, Ogbugo Ukoha, ya ce haramcin zai fara aiki daga 1 ga Maris din 2025, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 18 ga Janairu, wata fashewar tanker a Dikko, Jihar Niger, ta kashe akalla mutane 50 wanda ya kuma jikkata wasu da dama da raunuka masu tsanani.
Ukoha ya ce matakin na da nufin rage yawan hatsarurrukan manyan motocin mai da ke faruwa a hanyoyi.
An hana wasu tankokin mai hawa tituna
A taron manema labarai, Ukoha ya ce kwamitin fasaha na farko ya gana ranar Laraba don tsara hanyoyin aiwatar da matakan rage hadurran hanya.
Ya ce hukumomi da kungiyoyin da abin ya shafa sun halarta, ciki har da DSS, Hukumar gobara ta Kasa, da Hukumar Kiyaye Hadurra ta FRSC.
Haka nan, akwai NARTO, NUPENG, SON, DAPPMAN, da hukumar NMDPRA a cikin taron.
Ukoha ya ce daga 1 ga Maris, 2025, ba za a bari wata mota da ke ɗaukar fiye da lita 60,000 ta ɗauki kaya a kowanne sito ba, The Nation ta ruwaito.
"Abu mafi muhimmanci shi ne, mun cimma matsaya tare da duk masu ruwa da tsaki, kuma za mu ci gaba da aiki tare don tsaron hanyoyi."
- Ogbugo Ukoha
An samu gawarwaki bayan fashewar tanka
Kun ji cewa yawan mutane da suka mutu a gobara daga fashewar tankar fetur a Dikko da ke jihar Niger sai karuwa yake yi.
Aƙalla mutane da suka mutu sun kai 100, yayin da fiye da 50 suka jikkata, an kuma yi jana’izar gama-gari.
Gwamnan Niger, Mohammed Umar Bago, ya hana ababen hawa daga hanyar Maje amfani da gadar Dikko, yana mai nuna takaici.
Asali: Legit.ng