'Yan Shi'a Sun Fusata, Sun Aika Kakkausan Sako ga Gwamnatin Tinubu

'Yan Shi'a Sun Fusata, Sun Aika Kakkausan Sako ga Gwamnatin Tinubu

  • Kungiyar Shi’a ta bayyana cewa jami’an tsaro sun dakile taron Nisfu Sha’aban da suke shiryawa a Abuja don tunawa da ranar haihuwar Imam Mahdi
  • Shugaban kungiyar, Professor Abdullahi Danladi ya ce wasu jami’ai daga ‘yan sanda, sojoji, da DSS sun mamaye wurin taron da motocin yaki 50
  • Ya koka a kan abin da ya kira take masu hakki, da yin karan tsaye ga dokar Najeriya da ya ba su damar gudanar da taro a cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kungiyar 'Yan Shi'a a Najeriya (IMN) ta zargi jami’an tsaro da tarwatsa taron Nisfu Sha’aban a membobinta ke gudanarwa a Abuja.

Nisfu Sha’aban na daya daga cikin manyan abubuwan shekara-shekara da ake gudanarwa domin tunawa da ranar haihuwar Imam Mahdi, jikan Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

"Za mu kawo karshen mulkin kama karya," PDP ta musanta baraka a cikinta

Shi'a
Kungiyar shi'a ta fusata da jami'an tsaro Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, Farfesa Abdullahi Danladi, ya bayyana damuwarsu a cikin wata sanarwa da ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kungiyarsu ta kammala dukkan shirye-shirye akan taron an kammala su kafin ranar Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025.

Shi’a ta zargi sojoji da hana taron

Daily Post ta wallafa cewa Farfesa Danladi ya zargi tawagar motocin jami’an tsaro kimanin 50 sun isa wurin taron 'yan shi'a, dauke da jami’ai masu rike da manyan makamai.

Ya ce jami'an tsaron hadin gwiwar sun hada da jami’an ‘yan sanda (NPF), sojojin Najeriya (NA), DSS, da sauran su, inda suka mamaye wurin taron.

Ya ce:

"Jami’an tsaron sun fara takura wa mahalarta taron tare da umartar su da su watse, suna barazanar amfani da karfin gaske a kan mahalarta taron addini da ba su nuna wata tsokana ba."

Shi’a ta yi Allah wadai da sojoji

Kara karanta wannan

Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaron sun kafa hujjar cewa masu shirya taron ba su nemi izinin Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja ba kafin gudanar da taron.

Farfesa Danladi ya ce wannan ba huja ba ce, inda ya ce an nemi take ‘yancinsu na yin taro da kuma sabawa shari’ar kotu da ta tabbatar cewa ba dole ne a samu izinin ‘yan sanda ba kafin gudanar da taro cikin lumana.

"A bi mana hakkimu," Shi'a

Farfesa Danladi ya ce wannan tsangwama ta jefa mahalarta cikin damuwa tare da haifar da asara ta kudi da zamantakewa.

Ya kara da cewa:

"Muna bukatar a dauki matakin gurfanar da duk wadanda suka take mana ‘yancin ibadar addininmu. Mun kuma jaddada matsayarmu ta ci gaba da gudanar da ayyukan addini duk da tsangwamar jami’an zalunci."

Fadan shi'a ya hallaka 'yan sanda

A baya, kun ji cewa kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda 140 sun rasa rayukansu a shekarar 2024 sakamakon matsalolin tsaro da na lafiya.

CP Disu ya bayyana cewa wasu jami’an sun mutu yayin zanga-zangar ‘yan Shi’a da kuma sauran tashin-tashina a Abuja., wanda ke nuna irin hadarin da jami'an ke fuskanta a yayin gudanar da aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.