Matashi ya Gayyaci Abokinsa Gida Ya Masa Kisan Wulakanci da Adda, Ya Sassara Shi

Matashi ya Gayyaci Abokinsa Gida Ya Masa Kisan Wulakanci da Adda, Ya Sassara Shi

  • Wani matashi mai suna Iliayasu Mohammed ya halaka abokinsa, Safillahi Muhammad, bayan ya gayyace shi gidansa a Abuja ya bashi abinci
  • Rundunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa wanda ake zargin ya yi wa abokin nasa duka da adda sai da ya mutu
  • Bincike ya nuna cewa Iliayasu Mohammed tsohon bai laifi ne mai alaka da wata kungiya da ke satar babura a yankunan Abuja da kewaye

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta cafke wani matashi mai suna Iliayasu Mohammed bisa zargin kashe abokinsa, Safillahi Muhammad, da adda bayan ya bashi abinci.

Sanarwar da kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa an samu kiran gaggawa daga unguwar Dantata a Abuja kan wani mummunan kisan kai da ya faru.

Kara karanta wannan

Rumbun sauki: Gwamna ya bude wuraren sayar da abinci da araha ga talakawa

Abuja
An kama matashin da ya kashe abokinsa a Abuja. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton Punch ya nuna cewa jami’an ‘yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru misalin karfe 1:30 na rana a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, inda suka tarar da mamacin yana kwance cikin jini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda sun samu mamacin ya suma bayan munanan raunuka a kansa da jikinsa.

Yadda aka kashe Safillahi da arda

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa Iliayasu Mohammed ya gayyaci Safillahi Muhammad gidansa a unguwar Dantata, inda ya bashi abinci kafin daga bisani ya kai masa farmaki da adda.

Daily Post ta wallafa cewa Josephine Adeh ta ce:

“Bayan kiran gaggawa da muka samu a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, jami’anmu sun garzaya wurin da lamarin ya faru,
Sun kama wani matashi dan shekara 23 mai suna Iliayasu Mohammed daga yankin Dakwa a karamar hukumar Municipal, Abuja.
“Bincike ya nuna cewa wanda ake zargi ya janyo mamacin gidansa, ya bashi abinci, sannan ya kai masa hari da adda har sai da ya mutu.”

Kara karanta wannan

'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi

Adeh ta ce an garzaya da wanda aka kashe asibiti, amma likitoci suka tabbatar da cewa ya riga ya rasu.

Wanda ake zargi tsohon mai laifi ne

Bayanai sun tabbatar da cewa Iliayasu Mohammed tsohon fursuna ne da ke da alaka da wata kungiyar ‘yan daba da ke satar babura a Abuja da kewaye.

Adeh ta bayyana cewa yayin bincike, wanda ake zargi ya amsa laifinsa, tare da fallasa wasu mambobin kungiyar da ke karkashin jagorancin wani mutum mai suna Hassan.

Kakakin 'yan sandan ta ce:

“Mohammed ya bayyana cewa yana da alaka da wata kungiya da ke satar babura daga hannun 'yan acaba.
"Shugaban kungiyar, Hassan, har yanzu yana gudun hijira, kuma ‘yan sanda na ci gaba da bincike domin kamo sauran ‘yan kungiyar.”

Za a gurfanar da wanda ake zargi

Adeh ta tabbatar da cewa an riga an kama Iliayasu Mohammed, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da shi gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Kara karanta wannan

An gano dalilin faduwar farashi a shahararriyar kasuwar abinci a Kano

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja ya bukaci al’ummar birnin da su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton duk wasu ayyukan da ake zargin suna da nasaba da aikata laifi.

Rundunar ‘yan sandan FCT ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga 53 a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 53 a wani farmaki da suka kai a jihar Sokoto.

Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Dikko Umaru Radda ta yaba da kokarin sojojin tare da alkawarin cigaba da tallafa musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng