Ganduje Ya Kama Aiki a FAAN, Ya Kinkimo Babban Aiki a Filayen Jirgin Sama
- Dr. Abdullahi Ganduje ya kaddamar da ziyarar sa ta farko a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA) bayan nada shi sabn mukaminsa
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta nada Ganduje a matsayin shugaban kwamitin daraktocin hukumar filayen jirgin saman Najeriya (FAAN)
- Dr. Ganduje, wanda shi ne shugaban APC na kasa ya bayyana irin aikin da aka kudiri aniyar gabatar wa a kan dukkanin filayen jirgin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Shugaban kwamitin daraktocin Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN), Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya fara aiki a ofishinsa.
Yayin ziyarar sa ta farko a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA), Ganduje ya bayyana cewa akwai bukatar gaggawa ta inganta kayan aikin filin jirgin sama.

Kara karanta wannan
'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi

Asali: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa Ganduje ya fadi hakan yayin ziyarar duba aikin Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA), tare da Babbar Manajiyar FAAN, Mrs. Olubunmi Kuku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya amince da cewa yawancin kayan aiki da na'urorin filayen jiragen sama sun wuce yayi, kuma suna bukatar gyara da sabuntawa.
Ganduje zai jagoranci inganta filayen jirgin sama
FRCN ta wallafa cewa Dr. Abdullahi Ganduje ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki samun hadin kan kwamitinsa da shugabannin FAAN domin sabunta kayan aiki da gine-ginen filayen jirgin sama don su dace da ka’idojin duniya.
Ya ce:
“Akwai matsaloli da ke bukatar kulawa cikin gaggawa, amma mun fara tattaunawa kan yadda za mu magance su. Filayen jirgin sama a kasashen da suka ci gaba suna samun inganci ne ta hanyar ci gaba mai dorewa, shugabanci nagari, da saka hannun jari a sabbin fasahohi, wanda shi ne abin da muke son cimma.”

Kara karanta wannan
Dattawan Arewa sun yaba shirin Tinubu kan Arewa, sun tura muhimmin sako ga gwamnoni
Ganduje ya magantu kan ayyukan filayen jirage
Dr. Ganduje ya nuna damuwa game da wasu ayyuka da aka bayar shekaru da suka wuce da suka tsaya saboda hauhawar farashi da tasirin hauhawar kayan masarufi.
Ya kuma jaddada duk da haka, FAAN ta samar da tsarin da zai tabbatar a inganta kayayyakin da ake da su domin su yi kafada-da-kafada da takwarorinsu na duniya.
An fara ayyuka a filayen jirgin sama
Manajan Darakta a FAAN, Mrs. Olubunmi Kuku, ta ce an fara aikin gyara kayan aikin filayen jirgin sama a fadin kasar, kuma suna haifar da kyakkyawan sakamako.
Ta ce:
“Muna amfani da sababbin kayan gano abubuwan fashewa domin kara tsaro a filayen jiragen sama na kasar.
“Haka kuma, ana ci gaba da gyare-gyaren wurin saukar jiragen sama, kuma muna sa ran kammala wasu daga cikin ayyukan a cikin watanni masu zuwa.”
Tinubu ya nada Ganduje mukami
A baya, mun ruwaito cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nada shugabanni da daraktoci a hukumomi 42 na Gwamnatin Tarayya, ciki har da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje.
Daga cikin wanda aka yi wa nadin, akwai Nasiru Gawuna, wanda aka ba shi mukamin Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Asusun Ba da Lamunin Gidaje na Kasa (FMBN), kuma nadin ya fara aiki nan take.
Asali: Legit.ng