An Kashe Mutane 10, an Lalata Dukiyar Naira Biliyan 11 a Zanga Zangar Kano

An Kashe Mutane 10, an Lalata Dukiyar Naira Biliyan 11 a Zanga Zangar Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike kan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a Kano ranar 1 ga Agusta, 2024
  • Rahoton ya bayyana cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 7 suka jikkata sosai, tare da asarar dukiya ta sama da Naira biliyan 11
  • Gwamnatin Kano za ta fitar da takardar shaidar hukunci domin gano masu hannu a zanga-zangar da kuma aiwatar da shawarwarin kwamitin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin aiwatar da dukkan shawarwarin da kwamitin bincike kan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ya bayar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da yake karɓar rahoton kwamitin daga shugabansa, Mai Shari’a Lawan Wada (mai ritaya).

Kara karanta wannan

IBEDC: Duk da matsin rayuwar da ake ciki, an runtuma korar ma'aikata sama da 3,000

Abba Kabir
Abba Kabir ya karbi rahoto kan zanga zangar Kano. Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa
Asali: Facebook

Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Kano za ta hukunta duk masu hannu wajen lalata dukiya da jawo asarar rayuka a lokacin zanga zangar.

An rasa rayuka 10 a zanga zangar Kano

Rahoton kwamitin binciken ya bayyana cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 7 suka samu munanan raunuka a yayin zanga-zangar.

Haka zalika rahoton kwamitin ya nuna cewa an lalata kadarorin gwamnati da na ‘yan kasuwa da darajarsu ta haura Naira biliyan 11.

Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin sa ba ta yi katsalandan a binciken ba, don haka ya gamsu da sahihancin rahoton da kwamitin ya gabatar.

Matakin da Abba zai dauka kan rahoton

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa za a fitar da takardar shaidar hukunci domin gano masu hannu a zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Abba ya dauki mataki da ya ritsa malaman Kano sun saka dalibai leburanci

Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa za a hukunta wadanda suka haddasa asarar rayuka da dukiya a jihar.

Gwamnan ya yaba da aikin da kwamitin ya yi, yana mai cewa za a dauki matakan da suka dace domin dakile tashin hankali irin wannan a nan gaba.

Bayanin kwamitin binciken zanga zanga

Shugaban kwamitin binciken, Mai Shari’a Lawan Wada (mai ritaya), ya bayyana cewa sun ziyarci wuraren da abin ya shafa tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Mai Shari’a Lawan Wada (mai ritaya) ya bayyana cewa sun yi haka ne domin tattara bayanai kan yadda zanga-zangar ta faru.

Punch ta wallafa cewa rahoton su ya kunshi cikakken bayani kan illar zanga-zangar, tare da bada shawarwari kan matakan da gwamnati za ta dauka domin kaucewa irin haka a gaba.

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa aiwatar da wannan rahoto zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da adalci ga al’umma, tare da kare jihar daga sake fadawa irin wannan hali.

Kara karanta wannan

Dandazon jama'a sun tarbi Buhari da ya fito zabe na farko bayan gama mulki

Abba ya saka doka a makarantun Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya saka dokar hana sanya dalibai aikin karfi a makarantu.

Abba Kabir ya fadi haka ne yayin wata ziyarar ba zata da ya kai wata makaranta ya samu shugabannin makarantar sun sanya dalibai tonon rami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng