Mutum 25 Sun Kone bayan an Bankawa Kasuwar Zamfara Wuta
- Gobara mai muni ta tashi a kasuwar Talata Mafara, inda mutane sama da 25 suka jikkata wanda yanzu haka ake kokarin ceto rayuwarsu
- 'Yan kasuwar sun bayyana cewa suna zaune, kwatsam sai su ka ji harbe-harbe, sannan wata kara ta biyo baya, sai wuta ta tashi ganga-ganga
- Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara ta tabbatar da afkuwar gobarar, inda aka gano bindigar da ake zargin an yi harbe-harbe da ita a kasuwar
- 'Yan sanda sun ce ana cigaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin fashewar da kuma kama wadanda suka aikata lamarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar Talata Mafara dake jihar Zamfara, a ranar Talata, ta yi sanadin raunata mutane sama da 25.
Yanzu haka, mafi yawancin wadanda suka ji rauni suna karbar magani a Asibitin Kwararru na Talata Mafara a wani lamari da ya gigita jama'a.

Asali: Twitter
Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X cewa ce abin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na rana, yayin da 'yan kasuwa da masu siyayya suka ji harbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu fashewar abu a kasuwar Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa bayan harbe-harben ne, sai kwatsam aka ji karar abin fashewa wanda ya haddasa mummunan gobara da ta jikkata bayin Allah.
Wani dan kasuwar da lamarin ya rutsa da shi, ya bayyana cewa sun shiga halin rudani ganin yadda gobara ta biyo bayan fashewar wani abu.
Ya kara da cewa:
“Mun ji karar fashewa mai karfi sosai, sannan nan take wuta ta fara yaduwa cikin kasuwar da sauri. Mutane sun rika guduwa cikin tashin hankali, amma da dama sun makale cikin wutar.”

Kara karanta wannan
Adamawa: 'Yan ta'adda sun kai hari babban asibiti, an yi awon gaba da bayin Allah
‘Yan sanda sun tabbatar da gobara
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da gobarar, inda ta bayyana cewa mutane fiye da 25 sun jikkata bayan wutar ta ci jikinsu.
Rundunar ta tabbatar da cewa an garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa Asibitin Kwararru na Talata Mafara domin samun kulawa, amma ba a tabbatar da asarar rai ba tukunna.
An gano bindiga kirar Dane gun a wurin fashewar, amma babu wanda aka kama kawo yanzu, yayin da hukuma ta ce tana binciken lamarin don gano musabbabin fashewar da kuma gano masu hannu a aika-aikan.
Dan ta'adda na neman sulhu a Zamfara
A baya, mun wallafa cewa ana ta yada jita-jitar cewa rikakken dan fashi da shugaban kungiyar ta’addanci, Gwaska Dankarami, yana shirin tuba tare da mika wuya ga gwamnatin Najeriya.
Wannan batu ya taso ne tun bayan artabun da ya yi da wata kungiya karkashin jagorancin Sani Dangote a Zamfara, wanda ya jawo masa matsin lamba daga ‘yan kungiyar ta'addancinsa.
Gwaska Dankarami ya shahara a matsayin shugaba mafi girma a tsakanin ‘yan ta’adda da ‘yan fashi a Arewa maso Yamma, wanda ya sha jagorantar hare-haren da suka salwantar da rayuka.
Asali: Legit.ng