Muhimman Dalilai 4 da Suka Karya Farashin Abinci Ana Shirin Azumin Ramadan
Abuja - A ƴan makonnin nan farashin kayayyakin amfani na yau da kullum musamman hatsi na ƙara sauka a kasuwannin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wannan sauki dai na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar musulmi ke shirye-shirye fara azumin watan Ramadan, wata mai tsarki da albarka a musulunci.

Asali: Facebook
Daily Trust ta tattaro cewa a alƙaluman da hukumar kididdiga ta fitar a makon nan, hauhawar farashin kayayyaki ya yi gagarumar faɗuwa a ƙasar nan.
Alƙaluman sun nuna cewa yanayin hauhawar kaya ya rikito daga 34.80% a watan Disambar 2024 zuwa 24.48 a watan Janairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar NBS, farashin kayan abinci, makamashi da sauran kayayyaki ya karye sosai a farkon 2025 idan aka kwatanta da karshen shekarar 2024.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi tazari tare da tattaro muku nuhimnan abubuwan da suka taka rawa wajen karya farashin kayan abinci, ga su kamr haka:

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
1. Shigo da kayan abinci daga ketare
Babban dalilin da ake ganin ya sassauta tsadar kayan abinci irinsu masara, Gero. Dawa, shinkafa da sauransu shi ne wadatarsu a kasuwanni.
A rahoton da Punch ta wallafa, shugaban kasuwar Singer da ke Kano, Junaidu Zakari ya ce matakin da gwamnati ta ɗauka na ba ƴan kasuwa damar shigo da abinci ya taimaka wajen faɗuwar farashi.

Asali: Getty Images
Ya ce wasu daga cikin kayan da ake shigo da su sun hada da shinkafa, man girki, da taliyar leda, wanda hakan ya janyo raguwar farashin kayan abinci a Kano.
Ya jero yadda farashi ya karye, yana mai cewa shinkafa, wadda a baya ake sayar da ita kan N120,000, yanzu ta koma kasa da N80,000, yayin da taliya da aka sayar da uta kan N20,000 ta dawo N14,000.
2. Zuwan amfanin gona a (lokacin girbi)
Wani dalilin da ya rage tsadar kayan abinci shi ne albarkar da aka samu a noman bana da kuma manoma sun fara sayar da abubuwan da suka noma a kasuwanni.
Amfanin gona kamar dankali, tumatir da doya sun samu albarka sakamakon yanayi mai kyau da ruwan sama mai yawa da aka samu a daminar 2025.
Saboda yawaitar wadannan kayayyaki a kasuwa a karshen 2024 da farkon 2025, farashinsu ya ragu duk da dai manoma sun koka da hakan, in ji rahoton DW Hausa.
Wani ɗan kasuwa a Katsina, Malam Audu ya shaidawa Legit Hausa cewa yawan kayan abincin a kasuwa da kuma ƙarancin masu saye na ɗaya daga cikin abin da ya jawo karyewar farashi.
"Galibin magidanta suna sayen masara, dawa, wake da sauran hatsi a gida, ba sai sun je kasuwa ba, wani ma maƙocinsa ne zai sayar masa," in ji shi.

Asali: Facebook
3. Tsare-tsaren gwamnatin Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta dauki matakan rage hauhawar farashin kayan abinci. A 2024, ta dakatar da harajin shigo da kayayyakin abinci na wucin gadi, rahoton Reuters.
Wannan mataki ya taimaka wajen rage tsadar shigo da abinci daga kasashen waje, wanda ya haddasa gasa tsakanin ƴan kasuwa kuma ya sa farashi ya ragu.

Kara karanta wannan
'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai

Asali: UGC
Shugaban kasuwar Singer a Kano, Junaidu Zakari ya kara da cewa cire haraji kan wasu kaya guda 43 da shigo da shinkafa da ake sayarwa kan N40,000 ya taimaka wajen wadata kasuwanni da kayan abinci.
4. Farfaɗowar Naira a ƙasuwar canji
Rahoton Bussiness day ya nuna cewa bayan tsawon lokaci Naira na shan ƙasa a hannun Dalar Amurka a kasuwar hada-hadar kuɗin ƙetare, kuɗin Najeriya sun ƙara farfaɗowa.

Asali: Getty Images
A halin yanzu Dalar Amurka ta yi raga-raga, inda ta dawo ƙasa da N1,550 a kasuwar ƴan canji mako biyu bayan an yi cinikayyar kowace Dala kan sama da N1,600.
Wannan ya taimaka wajen rage tsadar shigo da kayayyakin abinci daga waje, wanda hakan ya taimaka wajen rage farashin abinci a cikin gida.
Yadda farashin ya sauka a kasuwa
Legit.ng Hausa ta bincika domin gano farashin abinci a kasuwar Ɗanja da ke garin Katsina kuma ta samu tabbacin sauƙin da aka samu.
Wani ɗan kasuwa, Malam Audu ya shaidawa wakilinmu cewa an samu ragi a mafi yawan kayan abinci idan aka kwatanta da watannin baya.
Ya ce buhun masara wanda a baya ya kai kimanin N70,000, yanzu ya sauka zuwa N50,000-N52,000, haka nan buhun dawa ya dawo N50,000.
Dangane da dalilin karyewar farashin, Malam Audu ya ce gaskiya wadatar abincin a kasuwa ne ya jawo haka, ya ce manoma ba su ji daɗin hakan ba duba da yadda suka sayi kayan gona da tsada.
"Eh tabbas an fara samun sauƙi, yanzu buhun masara da dawa duk kusan farashinsu ɗaya, N50,000 amma idan suna da kyau suna kaiwa har N52,000.
"Shinkafa sanfarera wacce ba a casa ba tana kai wa tsakanin N60,000-N70,000, ita ya danganta da wace iri ce da kuma yanayin kyaunta da auki idan an casa."
Haka nan, Nasiru Garba, wani mai shago ya shaidawa wakilinmu cewa a yanzu taliya ta sauka daga kimanin N20,000 zuwa N18,000.
"Shinkafa ƴar buhu ko nace maka yar gwamnati kamar yadda muka saba faɗa ta sauko zuwa N93,000 duk buhu ɗaya mai nauyin kilo 50," in ji shi.
Farashin abinci ya karye a Maiduguri
A wani labarin, kun ji cewa farashin kayan abinci a kasuwanni a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya ragu sosai yayin da mutane suka fara sayayyar azumi.
Wasu dai sun nuna farin cikinsu da wannan ci gaban yayin da wasu ke ganin akwai yiwuwa a ƙara samun sauƙi a gaba, hakan ya sa suka sayi kayan azumi kaɗan.
Asali: Legit.ng