IBEDC: Duk da Matsin Rayuwar da Ake Ciki, An Runtuma Korar Ma'aikata Sama da 3,000
- Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan a jihar Oyo (IBEDC) ya kori ma'aikata sama da 3,000 duk da halin matsin rayuwar da ake ciki
- Kungiyar kwadago watau NLC ta ɓarke da zanga-zanga, ta hana ayyukan kamfanin ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, 2025
- Shugaban NLC na Oyo ya buƙaci kamfanin raba wutar ya kira zaman tattaunawa domin magance matsalar cikin ruwan sanyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, Oyo - Kungiyar Kwadago reshen jihar Oyo (NLC) ta gudanar da gagarumar zanga-zanga a ranar Talata, inda ta tsayar da harkokin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan (IBEDC).
NLC ta gudanar da wannan zanga-zanga ne sakamakon korar ma’aikata sama da 3,000 ba tare da hujja ba a kamfanin IBEDC.

Asali: Facebook
Shugaban kungiyar NLC na Oyo, Kayode Martin, ne ya jagoranci zanga-zangar, suka toshe kofar shiga hedikwatar IBEDC a Ibadan, kamar yadda Punch ta kawo.

Kara karanta wannan
Ana zargin dan ta'adda da yan uwansa ke nema ruwa a jallo na neman sulhu da hukuma
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki ya haddasa cunkoson ababen hawa a yankin Challenge zuwa Dugbe da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Korar ma'aikata ta haddasa zanga zanga
Masu zanga-zangar, da ke rera wakokin nuna hadin kai, sun bukaci mayar da ma’aikatan da aka kora tare da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Shugaban NLC, Martin, ya soki kamfanonin da ke daukar ma’aikata a madadin IBEDC, yana mai zargin su da tauye hakkin ma’aikata ta hanyar kin biyan albashi.
"Mun fito yau domin nuna matukar kin jininmu kan zaluncin da kamfanin IBEDC da wakilansu ke yi wa ma’aikata.
"An kori ma’aikata sama da 3,000 ba tare da wani dalili ba. Wadannan mutanen sun sadaukar da lokacinsu da karfinsu ga wannan kamfani, amma yanzu an wurgar da su a matsayin marasa amfani," in ji Martin.
NLC da koka kan zaluntar ma'aikata
Ya kuma jaddada cewa kamfanonin daukar ma’aikata suna cin zarafin ma’aikata ta hanyar rashin biyan mafi karancin albashi da kuma cire kudi daga albashinsu ba tare da cikakken bayani ba.
"Ba za ta sabu ba, ba za mu lamunci irin wannan zalunci da cin zarafin ma'aikata ba," in ji shi.
Bukatu guda bakwai da NLC ta gabatar
Kungiyar ta gabatar da jerin bukatu bakwai ga mahukuntan IBEDC, wanda suka hada da, fara biyan mafi karancin albashi, biyan haƙƙokin fansho da maida ma'aikatan da aka kora.
Sauran bukatun sune, ba ma'aikata damar shiga NLC, kula da lafiya, biyan duk alawus da ma'aikata ke bi bashi da kuma daƙile wulaƙanci da wakilan kamfani ke yi.
Martin ya yi kira ga Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da sauran masu ruwa da tsaki su shiga cikin lamarin, yana mai gargadin cewa korar dubban ma’aikata na iya haddasa matsalolin tsaro.
Ya kuma bukaci mahukuntan IBEDC da su zauna teburin tattaunawa da kungiyar don magance matsalar cikin lumana kafin ta rikide zuwa wani mawuyacin hali.
Korarrun ma'aikta sun maka CBN a kotu
Kun ji cewa ma'aikata 1,000 da babban bankin Najeriya watau CBN ya kora daga aiki sun garzaya kotu, sun tuhumi bankin da karya dokoki.
Tsofaffin ma'aikatan sun shaidawa alkali cewa tsarin da aka buw wajen raba su da aikinsu ya saba doka, sun nemi kotu ta soke korar.
Asali: Legit.ng