Ana Zargin Dan Ta'adda da Yan Uwansa Ke Nema Ruwa a Jallo na Neman Sulhu da Hukuma
- Rahotanni sun nuna cewa hatsabibin dan fashi, Gwaska Dankarami, na shirin mika wuya bayan arangama da Sani Dangote a Zamfara
- Matsin lambar sojoji da rikicin cikin gida sun raunana ikon Dankarami, wanda ke haifar da jita-jitar mika wuyansa ga hukuma
- Ana zargin cewa wasu mayakansa sun fusata saboda dangantakarsa da Boko Haram, wanda ya haifar da rikici a cikin kungiyar 'yan fashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Gusau, Zamfara - Ana yada jita-jitar cewa rikakken dan fashi Gwaska Dankarami, yana iya shirin mika wuya ga hukuma.
Dan ta'addan wanda ya shahara a Zamfara da kai hare-hare na shirin haka ne tun bayan artabun da ya yi da Sani Dangote da kungiyarsa.

Asali: Facebook
Wanene rikakken dan ta'adda, Gwaska Dankarami?
Rahoton Zagazola Makama ya ce ana ta rade-radin cewa matsin lambar sojoji da rikicin cikin gida a kungiyar sun raunana ikon Dankarami.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwaska Dankarami ya kasance babban shugaba a tsakanin ‘yan fashi da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.
A ranar 7 ga Afrilun 2024, Dankarami da mayakansa sun kai hari kan bangaren Sani Dangote, Mallam, Saidu, da Lamo Saude a kauyen Dumburum, Zurmi.
Arangamar ta kashe ‘yan ta’adda 38 ciki har da Dangote wanda nasarar karfafa matsayin Dankarami a matsayin shugaban ‘yan fashi mafi iko a Zamfara.
Ana zargin Dankarami da alaka mai karfi da Boko Haram a yankin Arewa maso Yamma. Yana kuma jagorantar safarar makamai daga Nijar zuwa Najeriya, wanda ke kara tayar da tarzoma a yankin.
Ana hasashen Dankarami zai mika wuya
An ce hakan ya haifar da zancen mika wuyansa inda wasu ke ganin dabara ce ta yaudara da kuma gudun matsin lamba daga sojoji.
Ana ganin Dankarami na fuskantar matsaloli da suka hada da; ragowar magoya bayan Sani Dangote, ciki har da Alhaji Shingi da Alhaji Nashama, suna nemansa rai ko mace.
Jiragen sama masu leken asiri da hare-haren sojoji a maboyar ‘yan fashi a Zamfara da kewaye sun raunana ayyukan ‘yan fashi.
Ana kuma zargin cewa wasu mayakan Dankarami sun fusata da alakarsa da Boko Haram, wanda ya jawo rikici a cikin kungiya.
Sojoji sun hallaka kasurgumin dan ta'adda
Mun ba ku labarin cewa dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasarori a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a yankin Arewa maso Yamma.
An tabbatar sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka kwamandojin ƴan ta'adda a Sokoto da Zamfara.
Dakarun tsaron sun kuma lalata sansanonin ƴan ta'addan tare da ceto mutanen da suka yi garkuwa da su da dama yayin artabun.
Asali: Legit.ng