Magana Ta Kare, Kotu Ta Tabbatar da Fitaccen Sarki kan Kujerarsa bayan Rigimar Sarauta
- Kotun daukaka kara a Ibadan ta yi zama kan rigimar sarauta a jihar Oyo kan kujerar Soun na Ogbomoso
- Kotun yayin zamanta tabbatar da nadin Oba Ghandi Olaoye a matsayin Soun na Ogbomoso, bayan korafin da aka shigar kan zabensa
- A baya, kotun Oyo ta soke nadin, tana mai cewa ba a bi ka'idar dokar nadin Soun ba wajen zabensa
- Alkalin daukaka kara, Mai Shari'a, Nimpar, ya yi watsi da hukuncin kotun farko, wanda ya ba Oba Ghandi damar ci gaba da sarautarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ibadan, Oyo - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Ibadan a Oyo, ta yi zama kan rigimar sarautar jihar da aka dade ana yi.
Kotun ta tabbatar da zaben Oba Ghandi Olaoye, Orumogege III, a matsayin Soun na Ogbomoso da ke jihar Oyo.

Kara karanta wannan
'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi

Asali: UGC
Yadda kotu ta tsige Soun na Ogbomoso daga sarauta
Punch ta ruwaito cewa Mai Shari'a, Yargata Nimpar, wanda ya jagoranci kwamitin alkalai uku, shi ya yi hukunci, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin ya biyo bayan daukaka karar da Oba Ghandi ya shigar, inda duk kan dalilan 10 na karar suka ci gaba da goyon bayansa.
A baya, Mai Shari'a, K. A. Adedokun na kotun koli ta Oyo ya soke zaben Oba Ghandi a ranar 25 ga Oktoba, 2023, yana mai cewa an yi zaben ne ba bisa ka'ida ba.
Kotu ta tabbatar da nadin Soun na Ogbomoso
Kotun farko ta bayyana cewa ba a bi ka'idodin doka na nadin Soun ba wajen tabbatar masa da sarautar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sai dai kotun daukaka kara ta bakin Mai Shari'a, Nimpar ta soke hukuncin kotun farko, wanda ya ba Oba Ghandi damar ci gaba da mulki.
An maka gwamna a kotu kan rigimar sarauta
A baya, kun ji cewa rigimar sarauta ta dauki sabon salo bayan dan sarki, Ismaila Owoade ya garzaya kotu, yana son a soke nadin Prince Abimbola Owoade a matsayin Alaafin na Oyo.
Dan Sarkin ya yi korafin ne saboda yana zargin an nada shi ba bisa ka’ida ba inda ya ce bai kamata a nada wani ba tare da Baba Iyaji ya gabatar da sunan wanda ya dace ba.
Kotun ta sanya 11 ga Maris, 2025, don sauraren karar, yayin da Prince Gbadegesin ke kalubalantar matakin Gwamna Seyi Makinde.
Asali: Legit.ng