Adamawa: 'Yan Ta'adda Sun Kai Hari Babban Asibiti, An Yi Awon Gaba da Bayin Allah

Adamawa: 'Yan Ta'adda Sun Kai Hari Babban Asibiti, An Yi Awon Gaba da Bayin Allah

  • Rundunar 'yan sandan Adamawa ta tabbatar da cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace akalla mutane hudu a jihar
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da kai harin da aka kai asibitin koyarwa na Maodibbo
  • Ya tabbatar wa Legit cewa yanzu haka an aika dakaru har kashi biyu domin bin sahun 'yan bindigar da suka doshi iyakar Najeriya da Kamaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar AdamawaWasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mutane hudu, ciki har da jami'in lafiya daga Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, Yola.

Lamarin ya faru ne a kauyen Mayo Kila, wani yanki da ke kusa da iyakar Najeriya da Kamaru a karamar hukumar Jada ta Jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

Police
An sace mutum hudu a Adamawa Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa, harin ya auku ne da misalin karfe 1:30 na safe a ranar 17 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga, dauke da sun mamaye kauyen tare da yin garkuwa da mutanen, suka kuma yi gaba da su zuwa yankin tsaunuka da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Adamawa: An tabbatar da harin ‘yan ta’adda

Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 3:30 na safe, wanda hakan ya sa aka tura jami’an tsaro nan take domin daukar mataki.

Wata majiya daga ‘yan sandan ta ce:

"Muna samun rahoton, aka tura jami'ai wurin da lamarin ya faru, kuma an tura tawagar hadin gwiwa ta ‘yan sanda da mafarauta domin ganin an kubutar da mutanen da aka sace tare da kamo wadanda suka aikata laifin.”

Halin da ake ciki a Adamawa

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamna ya ɗaukaka kara, kotu ta bar mai martaba sarki kan mulki

Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa ta tura sashen yaki da garkuwa da mutane domin gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin, tare da kara tsaurara sintiri a yankin domin hana sake aukuwar irin wannan hari.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya shaida wa Legit cewa:

"Yanzu haka jami’anmu na can suna bin sahun wadanda suka yi garkuwa da mutanen. Haka kuma, jami’ai na kokarin kubutar da wadanda aka sace cikin gaggawa."

Ya zuwa yanzu, rundunar ba ta bayyana ko akwai wadanda suka ji rauni ba, amma ta tabbatar da cewa ana kokarin ganin an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su lafiya.

Najeriya ta yi babban rashi a Adamawa

A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yayi alhini kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Modibbo Ibrahim Daware, wanda ya rasu a jihar Adamawa.

A sanarwar da mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin sada zumunta, Dada Olusegun ya fitar, Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa bisa wannan babban rashi, tare da addu'ar ya samu rahamar Allah SWT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.