Saudiyya Ta Gwangwaje Kano da Abuja da Tallafi Mai Tsoka Albarkacin Watan Ramadan
- Gwamnatin ƙasar Saundiyya ta bai wa Najeriya tallafin dabino tan 100 domin rabawa mabuƙata albarkacin watan Ramadan
- Jakadan Saudiyya a Najeriya Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi ya ce tallafin za a raba shi ne tsakanin babban brnin tarayya Abuja da jihar Kano
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da al'ummar Musulmi ke shirye-shiryen fara azumin Ramadan nan da ƙasa da makonni biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta ba birnin tarayya Abuja da jihar Kano, tallafin tan 100 na dabino domin rabawa musulmi albarkacin watan Ramadana.
Wannan tallafi wani ɓangare ne na shirye-shiryen agaji da jin ƙai da Saudiyya ke gudanarwa domin taimaka wa al’ummar musulmi da sauran mabukata a faɗin duniya.

Asali: Twitter
NTA News ta ce Saudiyya ta ba jihar Kano tan 50 na dabino, sannan kuma ta ba Abuja tan 50 jimulla tan 100 kenan saboda gabatowar watan azumi.

Kara karanta wannan
Mubarak Bala da ƴan Arewa 4 da aka taɓa yankewa hukuncin kisa kan ɓatanci ga Annabi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ramadan: Saudiyya ta ba Najeriya dabino
Ƙasar ta ba da dabinon ne ƙarƙashin cibiyar agaji da jin ƙai ta Sarki Salman (KSrelief), wadda ke aiwatar da shirye-shiryen tallafi a duniya don rage wahala da bunƙasa jin daɗin al’umma.
Manufar wannan shiri na KSrelief shi ne tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi, ƙarfafa dangantaka da zumunci tsakanin Saudiyya da Najeriya da sauƙaƙa wa musulmi a lokacin azumin Ramadana.
A yayin miƙa tallafin a Abuja, Jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi, ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya ta himmatu wajen bda tallafi ga mabukata.
Yadda Saudiyya ke taimakawa musulmi
Ya jaddada cewa Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud na ci gaba da ƙoƙarin taimaka wa musulmi da sauran mabukata a duniya.
Faisal Al-Ghamdi ya ce Saudiyya na da ƙudurin ci gaba da haɗa kan musulmi tare da bayar da agaji ga marasa ƙarfi.

Kara karanta wannan
Kwana ya ƙare: Gwamna ya kaɗu da tsohon sanata ya riga mu gidan gaskiya a Najeriya
Yadda za a raba tan 100 na dabino a Najeriya
Daga cikin tan 100 na dabino, tan 50 za a miƙawa birnin Abuja yayin da sauran tan 50 za su tafi jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rabon dabinon zai bi tsarin tallafa wa mabukata da kuma inganta jin daɗin al’ummar musulmi a Najeriya.
Wannan tallafi ya kasance wani gagarumin shiri da Saudiyya ke gudanarwa kowacce shekara don taimaka wa musulmi albarkacin watan Ramadan.
Saudiyya ta ce manufar wannan shiri shi ne inganta rayuwar musulmi, rage wahala, da ƙarfafa haɗin kai, musamman a watan Ramadan wanda lokaci ne na ibada da kyautatawa ga juna.
Sai dai ƴan Najeriya na ganin ɗa wuya wannan tallafi da isa ga waɗanda aka ba da shi domin su.
Wani matashi, Abdullahi Tukur ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan ba shi ne karo na farko da Saudiyya ke ba Najeriya dabino ba amma ba ya isa ga al'umma.

Kara karanta wannan
"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha
A cewarsa:
"Saudiyya ta saba ba da wannan tallafi, zan iya cewa duk shekara, amma da wuya mahukunta su rabawa mutane ƙaso 20%, ni ban ma taɓa ganin irinsa ba.
"Fatana shi ne ko da ba a rabawa mutane kyauta ba a shigar da shi kasuwa yadda farashin dabino zai karye a watan Ramadan, mun fatan Allah ya karɓi ibadunmu."
Za a bunkasa noman dabino a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa da ke Arewa maso Yamma ta rattaɓa hannu kan yarjajeniya da wasu kamfanonin Sauidyya don bunƙasa noman dabino.
Hakan dai zai ba masana daga ƙasar Saudiyya damar amfani da fasahohin zamani domin haɓaka noman dabino a jihar Jigawa.
Asali: Legit.ng