Sojoji Sun Farmaki Maboyar Wani Babban Dan Bindiga, an Kashe 'Yan Ta'adda 53

Sojoji Sun Farmaki Maboyar Wani Babban Dan Bindiga, an Kashe 'Yan Ta'adda 53

  • Gwamnatin Katsina ta jinjinawa dakarun soji bisa nasarar kakkabe ‘yan bindiga a karamar hukumar Danmusa
  • Sojoji sun kai farmaki a maboyar babban dan bindiga, Kamilu Buzaru, inda suka hallaka mutum 53 daga cikinsu
  • Gwamnati ta bukaci al’umma su ci gaba da ba da hadin kai ga jami’an tsaro don dakile ayyukan ta’addanci a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin Jihar Katsina ta yaba wa dakarun rundunar hadin gwiwa ta sojojn Najeriya bisa kwazon da suka nuna a yaki da ‘yan bindiga a karamar hukumar Danmusa.

Sojojin sun kaddamar da farmaki a ranar 17 ga watan Fabrairu, 2025 kan sansanin wani shahararren jagoran ‘yan bindiga, Kamilu Buzaru, wanda ke zaune a tsaunin Dargaza.

Radda
Gwamnatin Katsina ta yabi sojoji bisa kashe 'yan ta'adda 53. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Ibrahim Kaulaha Mohammed ne ya wallafa yabon da gwamnatin ta yi ga sojoji a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dura kan 'yan bindiga suna shirin kulla alaka da Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa harin ya haifar da gagarumar nasara, inda aka halaka ‘yan bindiga 53 tare da rusa maboyarsu.

Sojoji sun kakkabe maboyar ‘yan bindiga

Bisa hadin gwiwar Rundunar Sojin Sama da ta Kasa, sojoji sun kai hari ta sama a maboyar ‘yan bindigar, inda suka fatattake su daga sansaninsu a tsaunin Dargaza.

Bayan kammala hari ta saman, dakarun kasa suka kutsa cikin sansanin domin tabbatar da cewa an kakkabe ‘yan bindigar gaba daya.

Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa farmakin babbar nasara ce ga yaki da ta’addanci a jihar, inda ya kawo cikas ga ayyukan ‘yan bindiga masu barazana ga zaman lafiya.

Sojoji sun sha yabo a jihar Katsina

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dr Nasir Muazu, ya bayyana cewa hadin gwiwar sojojin kasa da na sama ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ayyana neman fitaccen mawaki ruwa a jallo, sun gargadi al'umma

Ya ce harin da sojojin saman suka fara yi da jiragen yaki, sannan sojojin kasa suka shiga suka kammala aikin, ya nuna matakin jajircewa da kwarewa da dakarun tsaro suka nuna.

Gwamnatin jihar ta yabawa sojoji bisa irin kwazonsu da kuma yadda suka sadaukar da kansu domin tabbatar da cewa an murkushe ‘yan bindiga a yankin.

Gwamnati ta bukaci hadin kan jama’a

A cikin sanarwar, gwamnatin jihar ta bukaci jama’a da su ci gaba da ba da goyon baya ga jami’an tsaro ta hanyar ba su sahihan bayanai game da ayyukan ‘yan ta’adda.

Ta ce hadin gwiwar jama’a da jami’an tsaro shi ne hanya mafi dacewa don ganin an dakile ayyukan ta’addanci a jihar.

Gwamnati ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafawa jami’an tsaro da dukkan kayayyakin da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar.

Sojoji sun farmaki 'yan bindiga a Sokoto

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta yi magana kan zargin jefawa bayin Allah bam a jihar Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai mummunan farmaki kan 'yan bindiga a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Katsina.

Rahoton Legit ya nuna cewa sojojin sun kai farmakin ne a lokacin da 'yan ta'addar ke shirin kulla wata alaka da 'yan ta'addar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng