Farashin Kayayyaki Ya Yi Gagarumar Faɗuwa ana Shirin Azumin Ramadan a Najeriya
- Hukumar kididdiga ta ƙasa watau NBS ta ce an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a watan Janairu, 2025
- NBS ta bayyana cewa farashin kayayyaki ya yi gagarumar faɗuwa daga 34.80% a watan Disamba, 2024 zuwa 24.48% a watan Janairu, 2025
- Wannan dai na nuna cewa farashin kayayyaki kamar abinci sun sauka sosai idan aka kwatanta da yadda aka ƙarƙare shekarar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 24.48 cikin dari a Janairu 2025.
Wannan karyewar farashin kayayyaki na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Musulmi ke shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan na bana 2025.

Asali: Getty Images
Farashin kayayyaki ya karye a Najeriya
Rahoton Channels tv ya tattaro cewa farashin kayayyakin ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da kashi 34.80 da aka samu a watan Disamba na 2024.

Kara karanta wannan
'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar NBS na ƙasa, Adeyemi Adeniran, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, 2025 a wani taro a Abuja.
Ya ce ma'aunin CPI, wanda ake amfani da shi wajen auna sauyin farashin kayayyaki, ya ragu zuwa kashi 24.48 cikin dari a watan Janairun 2025.
Adeniran ya bayyana cewa:
"Hauhawar farashin kayayyaki a birane ya tsaya a kashi 26.09 cikin 100 yayin da farashin a karkara ya ruguzo zuwa 22.15%.
Ya kara da cewa farashin kayayyaki a kasa sun sauka sosai idan aka kwatanta da watan Disamba 2024, wanda aka yi amfani da tsohon tsarin auna hauhawar farashi.
Sabon tsarin ma'aunin CPI da tasirinsa
Sabunta ma'aunin CPI na nufin gyaran tsarin da ake amfani da shi wajen auna hauhawar farashi, domin ya fi dacewa da yadda mutane ke kashe kudinsu a yanzu.
A cewar sabbin alkaluman CPI:
"Hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 26.08% a watan Janairu, ma'ana dai ya ruguzo daga kashi 39.84% a watan Disamba, 2024.
"Sai kuma farashin kayayyakin da suka hada da farashin amfanin gona da makamashi, ya dawo kashi 22.59% a watan Janairun 2025.
A cewar NBS, sabon tsarin CPI ya fi nuna gaskiyar matsin tattalin arziki da yadda mutane ke kashe kudinsu a Najeriya.
Farashin abinci ya sauka a Kano
A wani labarin, kun ji cewa farashin kayan abinci a kasuwar Singer da je jihar Kano ya yi raga-raga, an ce farashin ya shafe kusan wata gudana yana sauka.
Shugaban kasuwar, Junaidu Zakari ya ce shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje na ɗaya daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen arahar da ake samu.
Asali: Legit.ng