An Kusa Shan Jar Miyan Pi, Dan majalisa ya Maka Shugaban Binance a Gaban Kotu
- Dan majalisar wakilai, Philip Agbese ya shigar da kara a gaban kotu bisa zargin shugaban Binance, Tigran Gambaryan da bata masa suna
- Shugaban kamfanin ya zargi Hon. Agbese da wasu 'yan majalisa uku da neman cin hanci a kan shari'ar da gwamnatin kasar ke yi da shi
- Lamarin ya sosa wa dan majalisar rai, wanda ke ganin ikirarin ya taba mutuncinsa ganin yadda ya ke da kima a idon mutanensa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Dan majalisar Wakilai, Philip Agbese, ya shigar da kara na N1bn a kan zargin bata suna da ya yi zargin shugaban kamfanin Binace, Tigran Gambaryan ya yi masa.
Shugaban Binance da ke fuskantar shari’a a Najeriya ya yi zargin cewa Agbese da wasu ‘yan majalisa biyu sun nemi cin hancin dala miliyan 150 daga gare shi.

Asali: Twitter
Premium Timesta ruwaito cewa dan majalisar shigar da karar a Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar karar na zargin cewa furucin da Gambaryan ya yi a shafukan sada zumunta sun danganta Agbese da cin hanci, lamarin da ke barazana ga mutuncinsa.
Dan majalisa na neman diyya daga shugaban Binance
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa dan majalisar na neman diyya ta N1bn a matsayin kudin da zai biya asarar da aka yi masa, da kuma naira miliyan biyar don biyan kudin shari’a.
An shigar da wannan kara ne sakamakon jerin rubuce-rubuce da Gambaryan, ya yi a shafukan sada zumunta, inda ya yi zargin cewa Agbese da wasu ‘yan majalisa na neman na goro daga wajensa.
Najeriya ta sake waiwayar shugaban Binance
A gefe guda, Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Kasa (FIRS) a ranar Litinin ta fara shari’ar da kamfanin Binance dangane da zargin kin biyan haraji.

Kara karanta wannan
Mawaki ya bijirewa mahaifiyarsa, ya koma soyayya da yar majalisa duk da gargadinta
FIRS ta gabatar da shaidarta ta farko, Mbami Shomgwan, wanda shi ne Manaja a sashen fasahar haraji na hukumar, a gaban Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Hukumar ta kuma yi garambawul ga karar da ta shigar, inda ta zargi Binance da gazawar tattarawa da biyan nau’ukan haraji daban-daban ga gwamnatin tarayya.
Zargin da Najeriya ke yi wa shugaban Binance
A sabuwar karar da FIRS ta shigar, ana zargin Binance da kulla hada-hadar kudaden intanet da kuma tura kudade ga ‘yan Najeriya ba tare da cire kudin VAT daga wadannan ayyuka ba.
An fara shari'ar ne bayan sanarwar da Binance ta fitar na nada wani dan Najeriya, Ayodele Omotilewa, a matsayin wakilinta, kuma tuni ya musanta zargin kin biyan haraji da ake yi masu.
"Yan majalisa sun nemi cin hanci," Binance
A baya, kun ji cewa shugaban kamfanin Binance, Shugaban kamfanin hada-hadar kudaden crypto, Binance, Tigran Gambaryan, yayi tonon silili a kan wasu 'yan majalisa kan zargin cin hanci.
Gambaryan ya bayyana Peter Akpanke, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Philip Agbese da Shugaban Kwamitin Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Ginger Obinna Onwusibe da neman ya ba su cin hanci.
Asali: Legit.ng