'Abin Ya Yi Muni': An Kashe Mutane 6 da Magoya bayan APC, PDP Suka Kacame da Fada

'Abin Ya Yi Muni': An Kashe Mutane 6 da Magoya bayan APC, PDP Suka Kacame da Fada

  • Rikici ya barke a Osun bayan hukuncin kotu da ake zargi ya mayar da shugabannin APC kan mukamansu, inda aka kashe mutum 6
  • Gwamna Ademola Adeleke ya zargi ministan tattalin arzikin ruwa, Gboyega Oyetola da jami’an tsaro da haddasa wannan rikicin
  • Shugaban 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya tura ƙarin jami’an tsaro don dakile rikicin, inda ya ce za a hukunta masu kitsa tashin tashinar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - An kashe mutane shida a jihar Osun biyo bayan rikicin da ya barke da kotu ta yanke hukuncin mayar da shugabannin APC kujerunsu.

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ce ta tabbatar da adadin mutanen da suka mutu yayin rikicin ga manema labarai a ranar Talata.

Gwamnan Osun ya zargi ministan Tinubu da hadda rikicin da ya jawo mutuwar mutane 6
'Yan sanda sun tura karin jami'ai Osun da rikicin siyasa ya jawo aka kashe mutane 6. Hoto: @AAdeleke_01, @officialABAT, @GboyegaOyetola
Asali: Facebook

Kakakin rundunar, Yemisi Opalola, ta shaidawa Channels TV cewa wadanda suka jikkata suna karɓar magani a asibitoci daban-daban a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi kunnen uwar shegu da gargadin Tinubu, zai gudanar da zabe a jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Osun ya zargi minista da haddasa rikici

Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya zargi ministan tattalin arzikin ruwa, Gboyega Oyetola, da wasu jami'an tsaro da haddasa wannan rikicin.

Gwamnan ya bukaci al'umma su kama Oyetola da shugabannin tsaron jihar da alhakin duk wani tashin hankali da zai biyo baya.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Yemisi Opalola ta ce:

“Abin da ya faru jiya ya yi sanadin mutuwar mutane shida, sannan da dama suna kwance a asibiti. Ba mu ji dadin wannan lamarin ba.
“Kafin wannan mummunan lamari, kwamishinan ‘yan sanda ya kira jam'iyyu daban-daban don tattaunawa kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya, amma abubuwa suka tabarbare.
“Wadanda ke haddasa wannan fitina su daina. Wannan jiha an santa da zaman lafiya, ba za mu bari wani ya dagula ta ba. Tawagar IGP ta iso daren jiya kuma an tura su aiki,” in ji ta.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi? APC ta sanar da ficewa daga zaben ƙananan hukumomi, ta jero dalilai

Ta jajanta wa wadanda abin ya shafa, tana mai bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi tare da alkawarin cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Sufeta Janar ya tura karin 'yan sandan jihar Osun

Sufeta Janar na 'yan sanda ya dauki mataki kan rikicin da ya barke a jihar Osun
Sufeta Janar na 'yan sanda ya tura karin jami'ai zuwa jihar Osun da aka kashe mutane 6. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Sufeta Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci a tura ƙarin jami’an tsaro Osun take domin tabbatar da tsaro da dawo da doka da oda a jihar.

IGP Egbetokun ya gargadi duk wanda ke ingiza tashin hankalin, yana mai cewa ba za su lamunci tarzoma ko rashin bin doka ba.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce shugaban 'yan sandan ya yi Allah wadai da rikicin da ya barke, yana mai cewa za a hukunta masu hannu a ciki.

Ya tabbatar da kudirin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da gurfanar da duk wanda ke da alhakin rikicin gaban shari’a.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara ɗaukar zafi, ana zargin IGP da shirya kashe gwamnan PDP a Najeriya

Osun: An kashe shugaban karamar hukuma

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu da ake zargin 'yan bangar siyasar PDP ne sun hallaka Mista Remi Abass, shugaban ƙaramar hukumar Irewole a jihar Osun.

Jam'iyyun APC da PDP na takaddama kan shugabancin ƙaramar hukumar, inda APC ke cewa kotun ɗaukaka ƙara ta mayar da shugabannin da aka sallama.

An yi musayar wuta yayin da 'yan bangar PDP suka kai farmaki ofishin shugaban karamar hukumar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Abass a take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.