Shin Gwamna Zai Cafke Mata da ba Su Sanya Rigar Nono ko Dan Kamfai? Gaskiya Ta Fito

Shin Gwamna Zai Cafke Mata da ba Su Sanya Rigar Nono ko Dan Kamfai? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin Anambra ta karyata jita-jitar kama mata da ba su saka rigar nono da dan kamfai a wuraren taruwar jama'a a jihar
  • An yada wani bidiyo a kafafen sada zumunta cewa Gwamna Soludo ne ya ba da umarnin kama matan
  • Kakakin gwamna ya ce labarin karya ne, mai cike da shiririta, kuma gwamnati ba ta tsoma baki a zaben tufafin jama'a ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Awka, Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta yi martani kan rahoton cewa za ta fara kama mata marasa rigar nono.

Gwamnatin ta karyata cewa za ta cafke mata da ba su sanya rigar nono ko dan kamfai a wuraren jama'a a jihar.

Gwamna ya ƙaryata shirin fara kama mata da ke yawo ba rigar nono
Gwamna Charles Soludo ya musanta cewa za a fara kama mata da ba su yawo da rigar nono. Hoto: Prof. Charles Soludo.
Source: Twitter

Yadda aka yada labarin kama mata a Anambra

Kakakin gwamnan, Christian Aburime, ya fitar da sanarwa cewa labarin yaudara ne kuma ana kokarin bata sunan gwamnati, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

'Ba ka isa ba': APC ta nunawa gwamnan Zamfara yatsa da ya haramta tarukan siyasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta a ranar Lahadi ya nuna cewa gwamnati za ta fara kama mata da ba sa sa kayan ciki.

A cikin bidiyon, an ji murya tana fadin cewa Gwamna Chukwuma Soludo ne ya ba da umarnin kama matan da ba su saka rigar nono.

"Wanda aka gani ba tare da rigar nono ko dan kamfai ba za a kama ta kuma a hukunta su."

- Cewar wata murya a bidiyo

Gwamnati ta musanta kama mata marasa rigar nono

Sai dai Aburime ya ce labarin karya ne, mai cike da shiririta, kuma gwamnati ba ta tsoma baki a zaben tufafin jama'a ba, Punch ta ruwaito.

Ya gargadi masu yada jita-jita da su daina, tare da kira ga jama’a su yi watsi da labarin domin ba gaskiya ba ne.

"Hankalin Gwamnatin Anambra ya karkata kan labarin karya da ke yawo a kafafen sada zumunta kan kama mata da ba sa saka rigar nono da dan kamfai.

Kara karanta wannan

Ramadan cikin sauki: Za a rabawa talakawa tirelolin abinci 500 kyauta a Neja

- Cewar sanarwar

Gwamnati ta gargadi al'umma kan yada labarin karya

Gwamnatin Charles Soludo ta bayyana cewa wannan labari karya ne kuma ana kokarin bata sunan gwamnati a idon jama'a.

Ko da yake gwamnati tana karfafa wa mutane guiwa domin saka suturar mutunci, ba ta tsoma baki a zaben tufafi ko kayan ciki ba.

Ta gargadi jama’a da su yi watsi da wannan labari na bogi kuma su tabbatar da sahihancin labarai daga kafofin gwamnati.

Masu yada wannan labarin karya su daina irin wannan saboda zai iya haifar da rudani da tashin hankali a cikin al'umma.

Yar TikTok ta ci wa malaminta mutunci

Kun ji cewa hatsaniya ta faru a sashen adabi na Jami’ar UNIZIK, Awka, bayan wata daliba ta kai wa malami hari tare da gartsa masa cijo.

An tabbatar cewa rikicin ya kaure ne lokacin da malamin ya katse dalibar a lokacin da take daukar bidiyon rawa na TikTok a harabar jami’ar.

Daga bisani, rahotanni sun tabbatar da korar dalibar daga karatu bayan kafa kwamitin wanda ya yi bincike mai zurfi kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.