Yan Bindiga Sun Karo Rashin Imani, Sun Kashe Mutane Kusan 20 a Garuruwa 2

Yan Bindiga Sun Karo Rashin Imani, Sun Kashe Mutane Kusan 20 a Garuruwa 2

  • Ƴan bindiga sun shiga kauyuka biyu a yankin ƙaramar hukumar Kwande ta jihar Benuwai, sun kashe mutane akalla 19
  • An tattaro cewa maharan sun yi ajalin manoma 16, sannan suka jefa gawarwakin su a kogi, lamarin da ya ƙara firgita mazauna yankunan
  • Rundunar ƴan sanda reshen Benuwai ba ta ce komai kan sababbin hare-haren ba amma shugabannin al'umma sun ce jama'a sun bar gidajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Mahara da ake zargin wasu makiyaya ne dauke makamai sun kai hare-hare a wasu kauyuka a karamar hukumar Kwande da ke jihar Benue.

Ƴan bindigar sun hallaka akalla mutane 19 da hare-haren da suka kai lokuta daban-daban a jihar Benuwai ƴan kwanakin nan.

taswirar Benue.
Yan bindiga sun shiga garuruwa, sun kashe mutane akalla 19 a Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yan bindiga sun kashe manoma 16

Rahoton Tribune ya ce a harin farko da aka kai ranar Asabar, an kashe manoma 16 da ke kan hanyarsu ta komawa gidajensu, inda aka jefa gawawwakinsu a cikin Kogin Katsina-Ala.

Kara karanta wannan

Mutumin da Tinubu ya naɗa a muƙami ya tsallake rijiya da baya, an yi yunƙurin kashe shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin Mbanduwa da bai so a ambaci sunansa ya ce:

“Manoman suna kan hanyarsu ta komawa kauyen Mbanduwa kwatsam maharan suka yi musu kwanton-bauna a daidai titin Kashimbila.
"Ƴan ta'addan sun kashe su, sannan suka jefa gawawwakin a cikin kogin Katsina-Ala.”

An kashe mutum 4 a hari na biyu

A hari na biyu da aka kai ranar Litinin da rana a kauyen Boaguwa, yankin Kumakua, cikin wannan karamar hukuma, maharan kashe mutum 3.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen yankunan da abin ya shafa sun fara guduwa daga gidajensu zuwa Jato Acka domin neman tsira da rayukansu.

Shugaban kungiyar Mzough U Tiv Worldwide, kuma jagoran kungiyoyin al’adu guda uku, Kwamfurola Iorbee Ihagh (mai ritaya), ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mutane sun fara barin gidajensu

“Ina cikin Jato Acka yanzu haka, an shaida min cewa an kashe manoma 16 a kan hanyar Kashimbila, sannan aka jefa gawawwakinsu a cikin Kogin Katsina-Ala.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin magoya bayan APC da PDP, an kashe mutum 2

“A yanzu haka, makiyaya sun sake kai hari a kauyen Boaguwa da ke Kumakua, kuma an gano gawarwakin mutum uku.
“Mutane sun gudu daga yankunansu suna neman mafaka a Jato Acka, wanda shi kansa garin ba wata cikakkiyar zaman lafiya ake ba."

- Iorbee Ihagh

Ya bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tura karin dakarun soji domin shawo kan matsalar, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Ƴan sanda ba su ce komai ba hare-haren

Duk wani kokari na jin ta bakin jami'ar hilɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan Benue, Catherine Anene, bai kao ga samun nasara ba domin ta katse wayar da aka yi mata.

Haka kuma, daraktan tsaron cikin gida na jihar Benue, Israel Gbawuam, bai samu amsa kiran da aka yi masa ba kan sababbin hare-haren ba.

Jami'an tsaro sun mukushe ƴan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa dakarun ƴan sanda sun kai samame, sun yi artabu da masu garkuwa da mutane a yankin karamar hukumar Kwande ta jihar Benuwai.

Dakarun sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga uku a samamen sannan suka ceto wani bawan Allah da aka yi garkuwa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262