Rundunar Sojoji Ta Yi Magana kan Zargin Jefawa Bayin Allah Bam a Jihar Katsina

Rundunar Sojoji Ta Yi Magana kan Zargin Jefawa Bayin Allah Bam a Jihar Katsina

  • Rundunar sajin saman Najeriya watau NAF ta fara gudanar da bincike kan zargin jefawa fararen hula bam a yankin Safana ta jihar Katsina
  • Hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya ba da umarnin yin bincike bayan samun rahoton cewa mutane bakwai sun mutu a harin jirgin soji
  • Rundunar ta ce jirgin ya kai hari ne kan wasu ƴan bindiga da suka farmaki jami'an tsaro, kuma an samu nasarar hallaka da dama daga cikinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ta yi magana kan zargin jefa wa fararen hula bam a Dutsen Yauni da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

An tattaro cewa harin jirgin saman ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai a ranar Asabar, 15 ga watan Fabrairu, 2025 a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin magoya bayan APC da PDP, an kashe mutum 2

Hafsan sojin sama.
Sojoji za su yi bincike kan zargin kashe fararen hula a Katsina Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

Rundunar sojoji za ta yi bincike

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin X yau Litinin, rundunar sojin saman ta ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin domin gano haƙiƙanin abin da ya auku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan hulɗa da jama’a na NAF, AVM Olusola Akinboyewa, ya ce Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Akinboyewa ya ce harin an kaddamar da shi ne domin dakile hari da ‘yan ta’adda suka kai wa ‘yan sanda da jami'an tsaron Katsina watau CWC.

Jirgin NAF ya farmaki ƴan bindiga

Ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirri kan ‘yan bindiga da suka fake a Dutsen Yauni, rundunar sojin ta aike da jiragen yaki don kai farmaki kansu.

"A lokacin farmakin, an gano ‘yan bindigan kuma an kai musu hari, tare da kashe da dama daga cikinsu," in ji shi.

Sai dai ya ce, bayan harin, an samu rahotanni masu tayar da hankali da ke cewa fararen hula sun rasa rayukansu a sakamakon harin, kuma hakan bai yi wa NAF daɗi ba.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun sake yin kuskure, sun hallaka bayin Allah a Katsina

Sojoji sun yi alkawarin gano gaskiya

"Kamar yadda muke bin ka’idojin aiki na kasa da kasa, muna sane da muhimmancin kare rayukan fararen hula," in ji Akinboyewa.

Ya ce rundunar ba za ta yi gaggawar yanke hukunci ba har sai an kammala bincike, tare da daukar matakin da ya dace.

Ya kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da binciken ke gudana, tare da tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kare rayukan fararen hula ba.

Sojojin sama sun kashe ƴan ta'adda a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta ci gaɓa da kai farmaki maɓoyar ƴan Boko Haram da nufin kakkaɓe ƴan ta'addan a jihar Borno.

A samameen wanda sojojin suka kai yankunan Degbewa da Chikide da Gwoza, sun yi nasarar tura ƴan ta'adda dama zuwa lahira tare da tarwatsa wuraren da suke ɓuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel