'Zaman Dadiro ba Kyau': Malamin Addini Ya Tara Jama'a, Ya Aurar da Mata 21 a Neja

'Zaman Dadiro ba Kyau': Malamin Addini Ya Tara Jama'a, Ya Aurar da Mata 21 a Neja

  • Shugaban cocin Katolika na Kontagora, Rabaran Dakta Bulus Yohanna, ya gudanar da bikin aurar da wasu masoya 21 a jihar Neja
  • Rabaran Yohanna ya jaddada muhimmancin aure cikin doka da ka'idar coci, yana mai cewa zama tare ba tare da aure ba babban laifi ne
  • Misis Cyprian Uche, wadda ta kwashe shekaru 22 da namiji, ta bayyana godiyarta ga coci saboda aurar da ita da aka yi a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Shugaban cocin Katolika na Kontagora, Rabaran Bulus Yohanna, ya gudanar da bikin aurar da wasu masoya su 21 a jihar Neja.

Taron ya gudana a cocin St. Mark a Nsanji Nkoso, cikin karamar hukumar Magama, inda aka daurawa masoyan aure bayan kammala kwas kan aure na watanni uku.

Shugaban cocin Katolika na Kontogora ya aurar da mata 21 a jihar Neja
Malamin addinin Kirista ya aurar da mata 21 da ke zaune da maza ba bisa aure ba. Hoto: Catholic Diocese of Kontagora
Asali: Facebook

Shugaban coci ya aurar da masoya 21 a Neja

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

Rabaran Yohanna ya bayyana cewa an yi taron auren ne don tabbatar da cewa masoyan suna zaman aure bisa doka a idon coci, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa har sai an yi aure a dokance da kiyaye ka'idojin coci sannan mace da namiji ke zama ma'auarata, inda ya ce yana da kyau a guji zama tare ba tare da aure ba.

Rabaran Yohanna ya bukaci ma'auratan su gina aure bisa kauna da juna, yana mai jaddada cewa aure yana nufin sadaukarwa na har abada.

Masoya sun yi godiya da aka aurar da su

Daya daga cikin ma'auratan, Mista da Misis Cyprian Uche, sun bayyana godiyarsu ga shugaban cocin saboda taimakon su wajen tabbatar da su a matsayin ma'aurata.

Mista da Misis Uche, wadanda suka kwashe shekaru 22 tare, har ma da yara guda biyar ba tare da aure ba, sun nuna farin cikin auren da aka yi masu a hukumance.

Kara karanta wannan

"Raba daidai ake yi," Gwamnatin Tinubu ta ce babu son rai a salon mulkinta

Misis Uche ta bayyana cewa yanzu tana da damar shiga kungiyar mata, wadda a baya ba ta samu damar ba saboda ba da aure take zaune da mijinta ba.

Malamin addinin Kirista ya aurar da ma'auratan da suka shafe shekaru suna zaman auren gargajiya
Malamin addinin Kirista ya tattara mabiyansa da ke zama tare ba da auren addini ba, ya daura masu aure. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mutane sun yi martani kan bikin aurar da matan

Singer Lampo:

"Gaskiya ka yi kokari fasto.. Faasto ya yi aikin azo a yaba. Ina da abokai kista da dama, suna son aure amma gaskyia suna yawan korafi a kan yadda auren su ya ke."

Ismail Usman

"Kai ku daina damun mutane fa. Aure a babin al' ada yake. Ko yaya aka daurashi ya dauru muddun an biya sadaki da shaidu."

Yakubu Tahir:

"Ai yanzu ma zaman dadiron ne, duk auren da ba na Musulunci ba, me ye bambancinsa da dadiron?"

Muslihu Ado Shehu:

"Gaba dayansu Allah ya shirye su, ya dawo da su hanya madaidaiciya, su shiga addinin Musulunci."

Dan majalisa zai aurar da 'yan mata 100

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Wani dan majalisar tarayya, Sani Yakubu Noma, ya shirya aurar da marayu mata 100 a jihar Kebbi.

Dan majalisar ya bayyana cewa shirin auren na daya daga cikin gudunmawar da yake bayarwa wajenkula jin dadin marayu a mazabar sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.