"Bai Dace Gwamnati Ta Nade Hannayenta ba": Ndume Ya Nemi Majalisa Ta Duba Zargi kan USAID
- Sanata Ali Ndume ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta binciki zargin dan majalisar Amurka, Scott Perry,
- Dan majalisa, Perry ya bayyana cewa Hukumar Bada Tallafin Raya Kasashe ta Duniya (USAID) ta na daukar nauyin ta'addanci
- Ndume na ganin bai kamata gwamnatin Najeriya ta yi biris da wannan babban zargi ba, ganin yadda aka illata Arewa da Boko Haram
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Dan majalisa mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta binciki zargin dan majalisar wakilai na kasar Amurka, Scott Perry.
Perry ya yi zargin cewa ana amfani da kudaden Hukumar Bada Tallafin Raya Kasashe ta Duniya (USAID) wajen tallafawa kungiyoyin ta’addanci, ciki har da Boko Haram.

Kara karanta wannan
Najeriya ta shirya dakile barazanar Trump, za a dauki ma'aikatan lafiya 28,000 aiki

Asali: Facebook
Da yake magana da Channels TV, Sanatan ya ce wannan ba wai zargi ba ne kawai, saboda haka ba daidai ba ne gwamnatin Najeriya ta yi shiru game da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume: “Majalisa ta binciki zargin USAID”
Punch ta ruwaito cewa Sanata Ndume, wanda ya kwashe fiye da shekaru 20 a majalisar, ya ce wajibi ne gwamnatin Najeriya ta dauki mataki a kan abin da dan majalisar Amurka ya bayyana.
Ya ce daukar matakin zai yi amfani ganin cewa an dade ana zargin wasu kungiyoyin agaji na kasashen waje da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya suna tallafawa ayyukan ta’addanci.
“Zargin abin damuwa ne,” Ndume
Sanata Ndume ya bayyana cewa Boko Haram ta yi fata-fata da rayuwar mazauna yankin Arewa maso Gabas a shekarun da aka kwashe ana kashe jama'a.
Sanatan ya ce:
“Za ku iya tuna yadda Boko Haram ta tada bama-bamai a hedkwatar ‘yan sanda da ofishin Majalisar Dinkin Duniya (UN) a Abuja, kuma asarar rayukan da aka yi ta yi yawa. Saboda haka, dole ne gwamnatin Najeriya ta nuna duba batun.
“Ina cikin damuwa, amma hukumomin tsaron Najeriya sun taba bayyana wannan ba kai tsaye ba a lokuta da dama. Har ma gwamnatin jihar Borno ta nuna taka tsantsan kan ayyukan wasu kungiyoyin agaji.
“Na tuna lokacin tsohon hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, sojojin Najeriya sun samu bayanai kan wannan har suka kai samame a ofishin USAID ko Majalisar Dinkin Duniya (UN) a Maiduguri. Akwai kuma lokacin da gwamnan ya samu bayanai, kuma hukumomin tsaro suka kai samame ofishin wata kungiya da ke koyar da ma’aikatanta yadda ake amfani da bindiga.”
Ndume ya magantu kan sukar Tinubu
A baya, mun ruwaito cewa Sanata Ali Ndume, wanda shi ne tsohon bulaliyar majalisa ya musanta cewa ya na gaba da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce ya na matukar mutunta jagoran.
Ya kara da cewa ya kan bayyana ra'ayinsa na matsin tattalin arziki da halin matsin rayuwa da talakawan Najeriya ke ciki, amma hakan ba ya nufin ya na gaba ko rashin daraja shugaban kasar.
Asali: Legit.ng