"Tinubu Sai Ya Zarce": Matawalle Ya Yi Martani ga Jami'in Gwamnatin Buhari
- Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa akwai dalilai masu tarin yawa da za su sanya Arewa ta sake zabar Bola Tinubu
- Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal kan yiwuwar Tinubu ya koma kujerarsa
- Matawalle na ganin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi a bangaren tsaro da tattalin arziki za su jawo masa tarin kuri'a daga shiyyar a zaben 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya yi martani ga tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, game da batun takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Matawalle, a wata sanarwa da Daraktan Bayanan Jama’a da Hulɗa da Jama’a na ma’aikatar, Henshaw Ogubike, ya fitar, ya jaddada cewa Tinubu ya samar da gagarumin ci gaba a shiyyar Arewa.

Asali: Facebook
This Day ta ruwaito cewa Matawalle ya nanata cewa tsohon SGF da abokan aikinsa za su yi mamakin irin goyon bayan da Tinubu zai samu daga arewa a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya fadi ayyukan Tinubu a watanni 19
The Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Matawalle ya jaddada cewa Tinubu ya yi ayyuka da dama, musamman a Arewacin Najeriya, tun bayan hawansa mulki.
Ya bayyana cewa:
“Shugaba Bola Tinubu, wanda bai wuce watanni 19 a kan mulki ba, ya samar da gagarumin ci gaba a dukkan sassan Najeriya, ciki har da Arewa. Mutanen Arewa za su mara masa baya domin ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ya fara.”
Tsaro: Matawalle ya jero nasarar gwamnatin Tinubu
Bello Matawalle ya bayyana wasu manyan sauye-sauyen Tinubu ya samar, wanda ya ya suka cancanci goyon bayan ‘yan Arewa, musamman a ɓangaren tsaro da kariya.
Ya ce:
“A shekarar 2024, dakarun tsaron Najeriya sun kashe fiye da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi 8,000, sun kama ‘yan bindiga da masu aikata laifi 11,600, kuma sun kwato fiye da makamai 10,000. Wannan matakin ya taimaka matuka wajen inganta tsaro a arewa."
“Arewacin Najeriya na nan daram ta na goyon bayan Shugaba Tinubu. Duk wani ƙoƙari na wargaza wannan goyon baya, yunkuri ne na haddasa fitina da kawo barazana ga tsaron ƙasa.”
Matawalle: “Akwai ci gaban tattalin arziki”
Ministan ya bayyana cewa an kafa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo na da nufin amfani da albarkatun noma a Arewa, haɓaka tattalin arziki da kuma inganta rayuwar miliyoyin mutane, musamman mata da matasa.
Ya ce:
“Wannan shiri zai sauya fasalin yankunan karkara kuma zai taimaka wajen samar da isasshen abinci. Faduwar farashin hatsi kwanan nan a faɗin ƙasa yana nuna tasirin manufofin noma na gwamnati.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa da suka shafi ci gaban tattalin arziki a Arewa, ciki har da gina sababbin tituna da inganta harkokin sufuri.
An gargadi Matawalle kan Amaechi
A wani labarin, mun ruwaito cewa jigo a APC a jihar Ribas, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya mayar da martani kan sukar da ƙaramin ministan tsaro, Dakta Bello Muhammed Matawalle, ya yi wa Amaechi.
Eze ya yi Allah wadai da gargaɗin da Matawalle ya yi wa tsohon ministan sufuri, yana mai cewa ya kamata a maida hankali kan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan maimakon yin barazana da ba ta da amfani.
Asali: Legit.ng