Ramadan Cikin Sauki: Za a Rabawa Talakawa Tirelolin Abinci 500 Kyauta a Neja

Ramadan Cikin Sauki: Za a Rabawa Talakawa Tirelolin Abinci 500 Kyauta a Neja

  • Gwamnatin jihar Neja ta ce za ta fitar da tireloli 1,000 na hatsi domin sayarwa a farashi mai rahusa a kananan hukumomi 25 da ke fadin jihar
  • Gwamna Umaru Bago ya ce kowace karamar hukuma za ta samu tireloli 10 a kowane kwana 10 a watan Ramadan, tare da tireloli 500 da za a raba kyauta
  • Gwamnatin za ta kafa kwamitoci biyu don kula da sayar da hatsi ga ma’aikata da sauran jama’a, tare da gargadin masu hannu da shuni da su guji cin amana

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ta bayyana matakin da za ta dauka domin rage wa al’umma wahalar abinci yayin azumin watan Ramadan.

Gwamnan jihar, Umaru Bago ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnati da ke Minna.

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

Umaru Bago
Gwamnan Neja ya dauki matakin karya farashin abinci a Ramadan. Hoto: Balogi Ibrahim
Asali: Facebook

Kakakin gwamna Bago, Bologi Ibrahim, ya wallafa a Facebook cewa gwamnatin jihar za ta tallafa wa al’umma ta hanyar samar da hatsi a farashi mai sauki domin rage radadin tsadar abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna bago zai raba abinci a Neja

Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa gwamnati ta samar da wadataccen abinci da zai wadaci jama’ar jihar Neja.

Ya ce kowace karamar hukuma za ta samu tireloli 10 na hatsi a kwanaki 10 na farko, na tsakiya da na karshen watan Ramadan domin tallafa wa jama’a.

Gwamna Umaru Bago ya kuma bayyana cewa za a raba tireloli 500 na hatsi kyauta ga marasa galihu a jihar.

A cewarsa, wannan matakin wani yunkuri ne na rage radadin tsadar abinci da ke addabar al’umma.

Kafa kwamitocin raba hatsi

Gwamnati za ta kafa kwamitoci biyu domin kula da sayar da hatsi ga jama’a cikin adalci da daidaito.

Kara karanta wannan

Birkin tirela ya tsinke a Kano, ta murkushe mutane da dama

Kwamitin farko zai kula da sayar da hatsi ga ma’aikatan gwamnati, yayin da na biyu zai hada da malamai, sarakuna da ‘yan kasuwa.

Gwamnan ya bukaci wadanda za a dorawa wannan nauyi da su ji tsoron Allah a yadda za su gudanar da aikin.

Ya kuma gargadi duk wanda aka samu da laifin cin amana ko karkatar da kayan tallafin za a hukunta shi ba tare da sassauci ba.

Ribar noma da aka samu a Neja

Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samu Naira biliyan 50 daga harkar noma da kiwo.

Ya ce hakan ya kara tabbatar da cewa noma na daya daga cikin manyan hanyoyin da za a bunkasa tattalin arziki a jihar.

Har ila yau, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ajiye Naira biliyan 5 daga ribar da ta samu domin gina asibitoci a jihar.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Gwamnan ya bukaci jama’a da su rungumi harkar noma domin cin moriyar albarkar da ke cikinta.

Wadanda suk halarci taron raba hatsin

Taron da aka gudanar ya samu halartar shugabannin kungiyoyin malamai, shugabannin NLC, shugabannin kananan hukumomi da sarakunan gargajiya.

Har ila yau, wakilan jam’iyyar APC da kungiyoyin ‘yan kasuwa sun halarci taron domin tattaunawa kan yadda za a aiwatar da shirin.

Gwamna Bago ya ba Izala N10m

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya ba kungiyar Izala da Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ke jagoranta N10m.

Umaru Bago ya ba kungiyar kudin ne a wani taro da Izala ta shirya domin neman N1.5bn na bunkasa harkokin ilimi a birnin tarayya, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng