Sojojin Sama Sun Sake Yin Kuskure, Sun Hallaka Bayin Allah a Katsina

Sojojin Sama Sun Sake Yin Kuskure, Sun Hallaka Bayin Allah a Katsina

  • An shiga jimami a jihar Katsina bayan dakarun sojojin saman Najeriya sun jefa bam bisa kuskure kan fararen hula
  • Bam ɗin wanda jiragen yaƙi na sojoji ya jefa, ya jawo asarar rayukan mutum bakwai tare da raunata wata mata a ƙaramar hukumar Safana
  • Sojojin sun jefa bam ɗin ne bayan ƴan bindiga sun hallaka jami'an ƴan sanda a wani artabun da suka yi yayin da suka yi yunƙurin kawo hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Dakarun sojojin sama na Najeriya sun sake yin kuskuren jefa bam kan mutane a jihar Katsina.

Harin na sojojin saman ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula bakwai a ƙauyen Yauni, gundumar Zakka da ke ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Sojojin sama sun jefa bam bisa kuskure a Katsina
Sojojin sama sun jefa bam kan mutane bisa kuskure a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Katsina

Jaridar Daily Trust ta ce, kafin wannan lamarin, an kashe wasu jami'an tsaro uku, ciki har da ƴan sanda biyu da kuma mamba na rundunar KCWC, yayin musayar wuta da ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun nuna kwarewa, sun cafke mambobin Boko Haram a cikin gari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2025.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindiga sun shirya kai hari kan masu kaɗa ƙuri'a a ƙauyen Zakka.

Sai dai, bayan samun labarin mummunan shirin, jami'an tsaro sun yi gaggawar ɗaukar matakin hana aiwatar da shi, wanda hakan ya haifar da musayar wuta tsakaninsu da ƴan bindiga,

A yayin musayar wutan, wani ɗan sanda da kuma mamba na rundunar KCWC sun rasa rayukansu, yayin da daga baya wani ɗan sanda da ya ji rauni ya rasu.

Jirgin sojojin sama ya jefa bam kan fararen hula

"Bayan wannan al'amari ne jirgin yaƙin sojoji, wanda ake tunanin ya zo domin ba da taimako, ya jefa bam a ƙauyen Yauni, da ke a Kudu da Zakka, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida ƴan gida ɗaya, yayin da wata mata ta ji rauni."

Kara karanta wannan

Shugaban Binance ya buɗe baki, ya jero sunayen ƴan Majalisa 3 da suka nemi cin hanci

- Wata majiya

Wannan ba shi ne karo na farko da mazauna jihar Katsina ke rasa rayukansu sakamakon hare-haren da sojojin sama ke kai wa bisa kuskure.

A watan Yuli, 2022, aƙalla mutane biyu sun rasa rayukansu bayan jirgin yaƙin sojoji ya jefa bam a ƙauyen Kunkunni, cikin ƙaramar hukumar Safana.

Ƙoƙari jin ta bakin jin ta bakin ƴan sanda da sojoji kan harin na ranar Asabar ya ci tura.

Sojojin sama sun hallaka fararen hula a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayukan mutane da dama yayin da wasu suka samu munanan raunuka sakamakon wani hari da jirgin yaƙin sojojin sama ya kai a jihar Sokoto.

Lamarin dai ya auku ne a ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

An dai tura jirgin yaƙin ne domin kai farmaki kan ƴan ta'addan Lakurawa, amma sai ya yi kuskuren aukawa kan fararen hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng