Dakarun Sojoji Sun Yi Artabu da Wasu Hatsabiban 'Yan Bindiga, An Kashe Miyagu

Dakarun Sojoji Sun Yi Artabu da Wasu Hatsabiban 'Yan Bindiga, An Kashe Miyagu

  • Sojojin OPSH sun kashe masu garkuwa da mutane biyu a Jema’a, Kaduna, bayan sun kai dauki don ceto fasinjoji da aka sace
  • A farmakin da aka kai dajin Angwan Rimi, sojoji sun kwato bindigar AK-47, harsasai takwas, wayoyi 10, da tsabar kudi N1,136,000
  • An ceto mutum uku da aka sace, ciki har da Mathew Ayemowa, Tunde Salam da Mustapha Mohammed, bayan artabu da ‘yan bindiga

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Sojojin Operation Safe Haven (OPSH) sun kashe masu garkuwa da mutane biyu tare da ceto mutum hudu a karamar hukumar Jema’a, Jihar Kaduna.

Majiyoyi sun bayyana cewa a ranar 14 ga Fabrairu, da misalin karfe 8:30 na dare, 'yan bindiga suka kai hari kan fasinjoji a yankin Afana Daji.

Sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga a dajin Kaduna, an ceto mutane hudu
Sojoji sun yi artabu da 'yan bindigar da suka farmaki matafiya, an kashe miyagu 2. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Kaduna

Kara karanta wannan

"Muna lalata da sama da maza 12 a rana": An ji ta bakin 'yan mata da ke karuwanci

Rahoton Zagazola Makama da ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna cewa sojoji sun kai dauki, inda suka ceci mutum daya da aka harba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce bayan ceton wannan fasinjan, sojojin OPSH sun kuma kaddamar da farmaki a dajin Angwan Rimi don bin sahun 'yan bindigar.

A ranar 15 ga Fabrairu, aka ce sojoji sun yi artabu da ‘yan bindiga a dajin Angwan Rimi, inda suka kashe biyu daga cikinsu.

'Yan bindiga sun ceto ragowar mutum 3

Binciken da sojojin suka yi, ya kai ga gano bindigar AK-47, gidan harsasai daya, harsasai takwas, wayoyi 10, kayan abinci da kudi har N1,136,000.

Rahoton ya ce sojojin sun ceto ragowar mutum uku da aka sace, ciki har da Mathew Ayemowa, Tunde Salam da Mustapha Mohammed.

Wannan dai na zuwa ne yayin da sojojin Najeriya ke ci gaba da kai hare-hare a sansanonin 'yan ta'adda na Kaduna domin murkushe miyagun.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano barbashen jirgin sama da ya yi hatsari a Borno, an kashe mutum 72

Sojoji sun ceto mutum 2 daga hannun 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin Najeriya na Operation Safe Haven sun dakile shirin fashi da makami a karamar hukumar Sanga, Jihar Kaduna.

A farmakin dakile harin 'yan bindigar da suka kai, sun ceci mutum biyu da ‘yan fashi suka kai wa hari a wurare daban-daban ranar 11 ga Fabrairu, 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel