Tinubu Zai Kinkimo Bashin $300m daga Bankin Duniya, An Ji Abin da Zai Yi da Kudin
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kokarin samun bashin dala miliyan 300 daga Bankin Duniya don inganta tsarin kiwon lafiya
- Hukumar NCDC ce za ta aiwatar da shirin, yayin da ma’aikatar kudi za ta wakilci gwamnati wajen karbar bashin daga Bankin Duniya
- Bankin Duniya zai tantance shirin a Afrilun 2025, ya yanke shawarar bayar da bashin a Yulin 2025 domin fara aiwatar da shi a 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta nemi sabon bashin dala miliyan 300 daga Bankin Duniya don karfafa tsarin tsaron lafiya a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa bashin zai kasance karkashin jagorancin Hukumar Dakile Cututtuka ta Najeriya (NCDC), wacce za ta aiwatar da shirin.

Asali: Twitter
Najeriya na neman bashi daga Bankin Duniya
Ma'aikatar kudi ta tarayya ce za ta wakilci gwamnatin tarayya wajen karbar bashin, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar shafin Bankin Duniya, an tsara shirin ne don bunkasa hadin gwiwa da karfafa hanyoyin ganowa da dakile barkewar cututtuka a Najeriya.
Ana sa ran za a bayyana cikakken bayani game da bashin a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, yayin da shirin ke a kan matakin tsarawa.
Abin da za a yi da bashin $300m
Bankin Duniya zai duba yiwuwar amincewa da bashin a ranar 30 ga watan Yuli, 2025, bayan kammala nazari da tantancewa.
Rahotanni sun ce za a tantance shirin a ranar 14 ga watan Afrilu, 2025, sannan za a fara aiwatar da shi a shekarar kasafin kudi ta 2026.
Wani rahoto ya bayyana cewa shirin zai karfafa hanyoyin bincike, gaggawar dakile cututtuka, da inganta dakin gwaje-gwaje a fadin Najeriya.
Kudin da Bankin Duniya ya warewa shirin
Shirin na daga cikin kudirorin gwamnatin Najeriya na bunkasa kiwon lafiya da kare yaduwar cututtuka ta hanyar hadin gwiwa da kasashen yanki.

Kara karanta wannan
Tinubu ya ba da umarni a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, an ji inda za a tura su
Haka nan, za a samar da dakunan gwaje-gwaje na tafi da gidanka, da kuma girka wuraren tsafta, ruwa, da makamashin hasken rana don inganta kayayyakin kiwon lafiya.
Bankin Duniya ya ware dala miliyan 300 don shirin, wanda zai taimaka wajen karfafa shirin dakile cututtuka da inganta tsarin kula da lafiyar jama’a.
Tinubu ya karbo bashin $1.57bn daga Bankin Duniya
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin arayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta karɓi bashin $1.57bn daga Bankin Duniya.
A cewar Bankin Duniya, ya amince da bashin tun ranar 26 ga Satumba domin tallafawa wasu muhimman ayyuka uku da Najeriya za ta aiwatar.
Asali: Legit.ng