Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohuwar Ambasada Ta Yi Bankwana da Duniya
- An sanar da rasuwar tsohuwar Jakadiyar Najeriya a Trinidad da Tobago, Ambasada Nne Furo Kurubo, a Lagos tana da shekara 84
- Kurubo ta sadaukar da rayuwarta wajen hidimar jama’a, tana ba da gudunmawa ga cigaban Najeriya da gwamnatin Jihar Rivers
- Marigayiya Kurubo 'yar uwar tsohuwar shugabar hukumar SEC, Mrs Ndi Okereke-Onyiuke ce, kuma tana da alaka da jihohin Rivers da Imo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku
Ikeja, Lagos - Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Ambasada Nne Furo Kurubo, tsohuwar Jakadiyar Najeriya a Trinidad da Tobago.
Marigayiyar ta rasu ne a ranar Laraba 12 ga watan Janairun 2025 a birnin Lagos tana da shekara 84.

Asali: Facebook
An yi rashin tsohuwar jakada a Najeriya
Wannan sanarwar ta fito ne daga iyalan marigayi Birgediya Janar George T. Kurubo daga Masarautar Grand Bonny a Jihar Rivers, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, iyalan marigayi Eze Sir Daniel Okereke daga Okpala da Ngor Okpala a Jihar Imo sun tabbatar da labarin rasuwarta.
Kurubo ta kasance mace mai kishin kasa wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen hidimar jama’a da bayar da gudunmawa wajen cigaban Najeriya.
Gudunmawar da marigayiyar ta bayar a Najeriya
Ta yi aiki tare da gwamnatin Jihar Ribas da kuma Tarayyar Najeriya, inda ta taka rawa wajen kyautata harkokin diplomasiyya da cigaban kasa.
An kuma bayyana cewa marigayiyar ta kasance 'yar uwar Mrs Ndi Okereke-Onyiuke, tsohuwar Shugabar Hukumar Tsaro da Kasuwanci (SEC) ta Najeriya.
Ta fito daga manyan iyalai biyu daga Jihar Rivers da Imo, wadanda suka shahara wajen bayar da gudunmawa ga cigaban al’umma.
Ambasada Nne Furo Kurubo ta bar tarihin sadaukarwa da jajircewa a aikin gwamnati da kyautata alaka tsakanin Najeriya da kasashen duniya.
Leadership ta ce jama'a da dama sun bayyana jimaminsu kan rashin ta, suna masu addu’ar Allah ya jikanta da rahama.
Gwanatin jihar Kano ta yi rashin shugaban REMASAB
A baya, mun kawo muku cewa al'ummar Kano sun shiga alhini bayan rasuwar fitaccen dan siyasa, Ahmadu Haruna Zago, wanda aka fi sani da Ɗanzago.
An bayyana cewa an yi jana'izar marigayin a fadar sarkin Kano da misalin karfe 1:00 na ranar Alhamis 13 ga watan Janairun 2025 inda manyan mutane suka halarta.
Kafin rasuwarsa, Ɗanzago ya rike mukamin shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano (REMASAB) a bangaren tsaftar muhalli wanda Gwamna Abba Kabir ya nada shi.
Asali: Legit.ng