Tinubu Ya Yi Magana kan Takaddamar Filin BUK, Ya Aika Sako ga Gwamna Abba
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓo batun taƙaddamar da ake yi kan filin jami'ar BUK da unguwannnin da ke makwabtaka da ita
- Mai girma Bola Tinubu ya buƙaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya warware taƙaddamar filin wacce aka ɗauki shekaru ana yi
- Shugaba Bola Tinubu ya kuma taya ɗaliban jami'ar waɗanda suka kammala digiri na ɗaya da na biyu murnar kammala karatunsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan taƙaddamar filin da ake yi tsakanin jami'ar BUK da unguwannin da ke makwabtaka da ita.
Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya magance taƙaddamar da ake yi kan filin.

Asali: Twitter
Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Asabar a Kano yayin bikin yaye ɗalibai karo na 39 a jami’ar BUK, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙaramar ministar ilmi, Farfesa Suwaibu Ahmed, ce ta wakilce shi a wajen taron yaye ɗaliban na jami'ar.
Me Tinubu ya gayawa Gwamna Abba?
Shugaban ya buƙaci gwamnan da ya dauki matakin gaggawa ta hanyar ba da takardar mallakar filin jami’ar domin warware matsalar. Ya jaddada muhimmancin tabbatar da filin jami’ar.
Shugaba Tinubu ya aminta da cewa sabuwar harabar jami’ar ba ta da katanga. Ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta ware kuɗi don gudanar da aikin.
“Gwamnatin tarayya ta riga ta samar da kuɗaɗen, kuma za a fara aikin."
- Shugaba Bola Tinubu
Ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta gine-ginen jami’o’i a faɗin ƙasar nan.
Shugaban ƙasan ya taya murna ga ɗalibai 3,400 na jami'ar da suka kammala karatun digiri na biyu.
Hakazalika ya yabawa ɗalibai 8,769 da suka kammala digirinsu na farko a makon da ya gabata.
Tinubu ya samu yabo
Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Abbas, ya jinjinawa Tinubu bisa kafa hukumar NELFund, wacce ke ba da rancen kuɗi ba tare da ruwa ba ga dalibai masu ƙaramin ƙarfi, don tallafa musu.
Hakazalika, Sagir Abbas ya yabawa Tinubu bisa cire jami’o’in tarayya daga tsarin IPPIS, wanda hakan ya dawo da ikon jami’o’in wajen daukar ma’aikata da biyan albashinsu.
Tinubu ya yi wa manyan Arewa laifi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi magana kan laifin da wasu manyan ƴan Arewa suke jin Bola Tinubu ya yi musu.
Ismaeel Ahmed ya bayyana cewa wasu manyan Arewa na jin cewa Shugaba Tinubu ya ajiye su a gefe, duk kuwa da irin ƙoƙarin da suka yi masa a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng