Mawaki Ya Bijirewa Mahaifiyarsa, Ya Koma Soyayya da Yar Majalisa duk da Gargadinta

Mawaki Ya Bijirewa Mahaifiyarsa, Ya Koma Soyayya da Yar Majalisa duk da Gargadinta

  • Duk da gargadin mahaifiyar mawaki, Innocent Idibia, an gano shi yana siyayya da Natasha Osawaru wanda 'yar majalisa ce a Edo
  • Iyayen 2Baba sun nuna damuwa kan alakar sa da Natasha, suna zargin cewa ba shi da cikakken hankali tun bayan rabuwar aurensa
  • Mahaifiyar 2Baba ta roki Natasha ta cire abin da ta saka masa, tana cewa yana bukatar 'yanci daga tasirinta bayan sakin da Annie Idibia
  • Hakan ya bayan bidiyon da ya nuna yana neman aurenta ya yadu a dandalin sada zumunta na zamani wanda ya jawo maganganu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Shahararren mawakin Najeriya, Innocent Idibia ya shiga shagon siyayya da budurwarsa yar majalisa.

Mawakin wanda aka fi sani da 2Baba, ya jawo ce-ce-ku-ce kan alakar sa da Natasha Osawaru, mataimakiyar shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

Mawaki ya ci gaba da soyayya da yar majalisa
Mawaki 2Baba ya yi fatali da gargadin mahaifiyarsa inda ya ci gaba da soyayya da yar majalisa. Hoto: @official2baba @Honorableosawaru.
Asali: Instagram

Mahaifiyar 2Baba ta gargadi 'yar majalisa

Wannan ya biyo bayan damuwar da iyalansa suka nuna game da inda yake da kuma alakarsa da 'yar majalisar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifiyarsa, Rose Idibia, ta yi kira ga Natasha da ta nesanta kanta da shi, musamman tun da har yanzu ba a kammala shari'ar rabuwar aurensa da Annie ba.

Rose ta yi ikirarin cewa danta ba ya cikin hayyacinsa sosai, tana zargin cewa abin da Natasha ta saka masa na tasiri a kansa, The Nation ta ruwaito.

Ta roki Natasha da ta cire kayan don ta 'yantar da shi, tana mai cewa:

“Na san dana sosai. Wannan ba shi ba ne.”

2Baba ya koma wurin yar majalisar Edo

An ga bidiyonsu suna siyayya tare a shagon kayan gyaran gashi, kwana kadan bayan labarin cewa iyalan mawaki 2Baba sun kai kara ga DSS suna cewa ya bace.

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

Wannan alaka ta 2Baba da yar majalisa ya jawo magana yayin da wasu ke ganin sakin tsohuwar matarsa na da alaƙa da soyayyar yar majalisar.

2Baba ya kamu da soyayyar yar majalisa

A baya, kun ji cewa fitaccen mawaki a Najeriya, Innocent Idibia, ya sanar da alakar soyayyar da ke tsakaninsa da ‘yar majalisar jihar Edo, Natasha Osawaru.

Hon. Natasha wacce ita ce mataimakiyar shugaban masu rinjaye a majalisar Edo, ta ja hankalin mutane bayan bullar hotuna da bidiyonta da 2Baba.

A cikin wani faifan bidiyon da ya yadu, 2Baba ya ce Natasha ba ta da alaka da rabuwarsa da Annie Idibia kuma yana son 'yar majalisar da aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.