Gwamna Ya Umarci Ciyamomi Su Fara Biyan Albashin N85,000 ga Ma'aikatansu

Gwamna Ya Umarci Ciyamomi Su Fara Biyan Albashin N85,000 ga Ma'aikatansu

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya umarci shugabannin kananan hukumomi su fara biyan mafi karancin albashi na N85,000 a Rivers
  • Fubara ya bukaci Kwamitin Hidimar Kananan Hukumomi su kawar da sunayen ma’aikatan bogi don rage nauyin biyan sabon albashin
  • Mai girma Gwamnan Ribas ya jaddada mahimmancin karin girma ga ma’aikata tare da tabbatar da da’a da inganci a aikin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Port Harcourt, Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers ya ba shugabannin kananan hukumomi umarni kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Fubara ya umarci su fara aiwatar da biyan mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatansu.

Gwamna ya umarci fara biyan ma'aikatan ƙananan hukumomi N85,000
Gwamna Siminalayi Fubara ya bukaci shugabannin kananan hukumomi su fara biyan mafi ƙarancin albashin N85,000. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Twitter

Albashi: Gwamna Fubara ya ba ciyamomi umarni

Fubara ya yi wannan jawabi ne a gidan Gwamnati, bayan kaddamar da shugabanni da mambobin Kwamitin Hidimar Kananan Hukumomi, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Dandazon jama'a sun tarbi Buhari da ya fito zabe na farko bayan gama mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bukaci sababbin shugabanni da mambobin Kwamitin su taimaka wajen aiwatar da sabon albashin tare da shugabannin kananan hukumomi.

Ya kuma kaddamar da shugaba da mambobin Kwamitin Hidimar Majalisar Dokokin Jihar Rivers (RSHA).

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labaransa ya fitar, Fubara ya umarci kananan hukumomi su fara biyan sabon albashin N85,000 ga ma’aikatan su.

Ya ce umarnin ya jawo korafe-korafen kasancewar akwai sunayen ma’aikatan bogi ko karin sunaye da ke bukatar bincike sosai.

“Dole ku taimaka wa shugabannin kananan hukumomi wajen kawar da sunayen bogi don rage nauyin biyan sabon albashin.
“Ba na nufin a kora ma’aikatan gaskiya ba ne, a tabbatar cewa duk wanda ke cikin sunayen ya cancanci albashi.”

- Cewar sanarwar

Gwamna ya bukaci bincike kan ma'aikata

Fubara ya kuma umarci kwamitin su magance matsalar tsaikon karin girma ga ma’aikata tare da tabbatar da da’a a ayyukan gwamnati.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnati za ta ba su goyon bayan da suke bukata wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Gwamna ya bukaci jiragen yaki su rika sintiri a iyakokin Bauchi

Ya kuma yi kira ga Kwamitin Hidimar Majalisar Dokoki su tabbatar da ingantaccen aiki da da’a a ayyukan majalisar dokokin jihar.

Fubara ya gargadi sababbin shugabanni su tabbatar da cikakken iko da da’a a ayyukan su.

Gwamna ya jika ma'aikata da sabon albashi

Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde na Oyo ya sanya ma'aikatan jihar murna bayan an fara biyansu sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000.

Gwamnatin jihar Oyo ta cika alƙawarin da ta dauƙa na fara biyan ma'aikatan sabon mafi ƙarancin albashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel