'Yan Sanda Sun Nuna Kwarewa, Sun Cafke Mambobin Kungiyar Boko Haram a Cikin Gari
- Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Gombe sun samu nasarar cafke wasu da ake zargin mamboboin ƙungiyar Boko Haram ne
- Ƴan sandan sun cafke mutanen ne guda biyu a cikin wani otal bayan sun samu bayanan sirri kan ayyukansu
- A yayin samamen da aka kai kan waɗanda aka zargin, an ƙwato kuɗaɗe, layu tare da kayan sawa a cikin wata baƙar jaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Gombe - Rundunar ƴan sanda ta jihar Gombe ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da kasancewa ƴan ƙungiyar Boko Haram.
Ƴan sandan sun cafke mutanen ne waɗanda ake kyautata zaton suna da hannu a harin da aka kai garin Garkida da ke ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa a cikin ƴan kwanakin nan.

Asali: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun cafke ƴan Boko Haram a Gombe
Majiyoyi sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun haɗa da Abubakar Mohammed, mai shekara 22, da Abubakar Usman, mai shekaru 20.
Dukkanin mutanen biyu mazauna unguwar Lawanti ne a ƙaramar hukumar Akko da ke jihar Gombe.
Ƴan sanda sun cafke waɗanda ake zargin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu, da misalin ƙarfe 1:00 na dare, a otal ɗin Rocket Hotel, New Mile 3, da ke kan hanyar Yola.
Jami’an tsaro na Operation Hattara ne suka gudanar da samamen bayan samun sahihan bayanai daga 'yan ƙungiyar (ADS Hunters Group), waɗanda suka haɗa da Abubakar S. Gombi da Umar Bukar.
Bayan binciken da aka gudanar a kan mutanen da ake zargin, an samu kuɗaɗe har N63,000, layu da wasu kayan sawa na maza a cikin wata baƙar jaka. Sai dai ba a samu wani makami ba yayin kamen.
An miƙa waɗanda ake zargi hannun sojoji
Majiyoyin sun ce mutanen da ake zargin za a miƙa su ga rundunar sojoji ta 301 Artillery Regiment domin cigaba da bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Gombe ya gargaɗi jama’a da su yi taka tsantsan da baƙi da kuma duk wani abu da ka iya zama barazana ga zaman lafiya.
Ya kuma buƙaci haɗin kai daga jama’a domin ci gaba da kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta’adda a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.
Ƴan sanda sun kashe ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kebbi sun samu nasara kan miyagun ƴan bindiga a wani samame.
Ƴan sandan sun hallaka ƴan bindiga guda huɗu bayan sun yi artabu tare da cafke wani guda ɗaya daga cikinsu ɗauke da raunukan harbin bindiga.
Jami'an tsaron sun kuma ceto wani dattijo mai shekara 60 wanda ƴan bindigan suka sace a harin da suka kai a ƙaramar hukumar Suru ta jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng