'Yan Sanda Sun Yi Raga Raga da 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutumin da Suka Sace

'Yan Sanda Sun Yi Raga Raga da 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutumin da Suka Sace

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kebbi tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun samu nasara kan ƴan bindiga masu ɗauke da makamai
  • Ƴan sandan tare da ƴan bangan sun hallaka ƴan bindiga mutum huɗu bayan sun sace wani dattijo mai shekara 60 a ƙaramar hukumar Suru
  • Jami'an tsaron sun kuma cafke wani ɗan bindiga ɗaya tare da ceto mutumin da aka sace ba tare da ya ji rauni ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Jami'an ƴan sanda da ƴan banga sun samu nasarar kashe ƴan bindiga a jihar Kebbi.

Jami'an tsaron sun hallaka ƴan bindiga masu garkuwa da mutane guda huɗu tare da ceto wani mutum mai shekaru 60 a jihar Kebbi.

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga a Kebbi
'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga a Kebbi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun nuna kwarewa, sun cafke mambobin Boko Haram a cikin gari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun ragargaji ƴan bindiga

Majiyoyi sun bayyana cewa jami'an tsaron sun kai farmakin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu, da misalin ƙarfe 1:45 na rana.

Ƴan sandan sun kai ɗauki ne lokacin da wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai suka farmaki ƙauyen Gobiraje da ke ƙaramar hukumar Suru, inda suka sace wani mazaunin garin mai suna Umaru Bawa daga gidansa.

Bayan samun rahoton wannan mummunan hari, DPO na Suru tare da tawagarsa ta ƴan sanda da ƴan banga, sun bi sahun masu garkuwa da mutanen zuwa cikin dajin Tundufai da ke yankin Dakingari.

A cewar majiyoyin ƴan sanda, jami’an tsaro sun yi gumurzu da ƴan bindigan, wanda hakan ya kai ga kashe hudu daga cikinsu, sannan suka cafke mutum ɗaya wanda yake ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Sai dai, wasu daga cikin ƴan bindigan sun tsere ɗauke da raunuka, amma jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin kamo su.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga bayan sun gwabza fada a Katsina

Ƴan sanda sun ceto mutumin da aka sace

A yayin wannan samame, jami’an tsaro sun samu nasarar ceto mutumin da aka sace ba tare da ya samu wani rauni ba.

Bugu da ƙari, jami’an tsaron sun karɓo kuɗin fansa har Naira miliyan uku da iyalansa suka riga suka biya masu garkuwa da shi.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kebbi ya yaba da kokarin jami’an tsaron, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro domin hanzarta daƙile ayyukan miyagu da ke addabar yankunansu.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Duk da yin sulhu, 'yan.bindiga sun tafka ta'asa a jihar Kaduna

Ƴan bindigan a yayin harin sun sace mutane fiye da 10 da suka haɗa da mata da yara, tare da ƙona gidaje da amfanin gona.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng