Jerin Jihohin Arewa da Za Su Yi Wa Matasa Auren Gata a 2025
Gwamnatocin wasu jihohin Arewa sun fara kawo tsarin auren gata ga matasa domin tallafa mus su raya Sunnah.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
A shirin dai, a kan zaɓo wasu mutane domin su amfana da tsarin wanda gwamnatocin suka fito da shi.

Asali: Twitter
Ra'ayi ya bambanta kan auren gata
Mutane dai suna bayyana mabambantan ra'ayoyi kan auren gata da wasu gwamnatocin jihohin Arewa suke gudanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai masu yi wa shirin kallon yana taimakawa wajen tallafawa matasa da suka gagara yin aure, samun damar yinsa a sauƙaƙe.
Ana yi wa shirin kallon hanyar rage matsalar zinace-zinace da ake fama da ita a tsakanin al'umma.
Sai dai, duk da hakan, akwai masu yi wa shirin kallon abin da bai dace ba domin a ganinsu ba shi abin da jama'a suka fi buƙafa ba.
A ganinsu biliyoyin kuɗin da ake warewa domin gudanar da shirin, za su yi amfani sosai idan aka tura su a ɓangarorin samar da ruwan sha, kiwon lafiya da sauran wurare masu muhimmanci da jama'a za su amfana da su.

Kara karanta wannan
Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook
Jihohin Arewa da za su yi auren gata
1. Jihar Kano

Asali: Facebook
Kamar yadda ta yi a shekarar 2024, gwamnatin jihar Kano ta sake faɗin shirinta na gudanar da auren gata a shekarar 2025.
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware biliyoyin kuɗaɗe domin gudanar da shirin na auren gata.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi na jihar Kano, Musa Shanono ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 2.5 domin gudanar da shirin a shekarar 2025.
Kwamishinan ya bayyana cewa an ware kuɗaɗen ne a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025, wanda majalisar dokokin jihar ta amince da shi.
Shirin na shekarar 2025, za a gudanar da shi ne a faɗin ƙananan hukumomin jihar guda 44.
2. Jihar Kebbi

Asali: Facebook
Jihar Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin da za a gudanar da auren gata ga matasa a shekarar 2025.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kebbi za ta gudanar da auren gatan ne a cikin watan Fabrairun 2025.
Shugaban kwamitin shirye-shirye, Alhaji Sulaiman Argungu ya bayyana cewa za a gudanar da auren ne ga mutane 600, da suka haɗa da amare 300 da angwaye 300.
Ya bayyana cewa wace amarya zata karɓi sadakin ta na N180,000 tare da gado da filo da sauran kayan ɗaki.
A cewarsa shirin auren gatan na shekarar 2025 zai mayar da hankali ne kan marayu, zawarawa, da mutanen da ke da buƙatu na musamman, ba tare da la’akari da ƙabilarsu ko addininsu ba.
Alhaji Sulaiman Argungu ya bayyana cewa za a gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar wata ƙungiya mai zaman kanta, watau Nafisa Nasir Charity Development Foundation (NANAS).
Ɗan majalisa zai aurar da ƴan mata 100
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓun Argungu/Augie daga jihar Kebbi, Sani Yakubu Noma, ya shirya aurar da ƴan mata guda 100.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito da ake raɗe raɗin shugaban AfDB na shirin kawo wa Tinubu cikas a 2027
Ɗan majalisar ya bayyana cewa zai aurar da ƴan matan ne guda 100 waɗanda gabaɗayansu suka kasance marayu ne.
Sani Yakubu Noma ya bayyana cewa aurar da ƴan matan da zai yi, na daga cikin gudunmawar da zai ba da wajen kula da jin daɗin marayu a mazaɓarsa.
Ya bayyana cewa an zaɓo ƴan matan ne daga cikin ƙananan hukumomi biyu da ya ke wakiƙta a majalisar wakilan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng